
A ranar 30 ga watan Mayun nan ne shugaban hukumar fasa kwauri ta kasa, Kanal Hameed Ali (retd) ya anwance da sabuwar amarya.
Shugaban kwastan din da ya rike mukamin kanal kuma ya rike mukamin gwamnan jihar Kaduna a lokaci soja a shekarar 1996 zuwa 1998, ya auro sabuwar amaryar tashi ne bayan rasuwar tsohuwar matarshi Hajiya Hadiza Jummai Ali, wacce ta rasu a ranar 29 ga watan Oktobar shekarar 2019 a babban birnin tarayya Abuja.
Auren wanda bai samu halartar mutane da yawa ba saboda halin da ake ciki na annobar coronavirus, an daura shi a jihar Kano, ga dai wasu daga cikin hotunan daurin auren:

