Hotuna: Shekaruna 30 amma har yanzu babu saurayi – Budurwa ta koka akan rashin tsayayyen saurayi

1
265
  • Budurwa ta koka matuka akan rashin saurayi bayan ta cika shekaru 30 a duniya
  • Budurwar ta wallafa hakane a shafinta na Twitter, inda ta bukaci Twitter ta nema mata saurayi
  • Ta ce aiki yayi mata yawa, saboda haka kada saurayi ko mijin da za ta aura yayi tunanin za ta dafa masa abinci ko kuma tayi wanki

Wani rubutu da wata kyakkyawar budurwa ‘yar Najeriya mai suna Oluwaseyi Funmi tayi a shafinta na Twitter ya jawo kace-nace.

Kyakkyawar budurwar da ta cika shekaru 30 a duniya ta wallafa wani rubut a shafinta na Twitter, inda ta bayyana cewa tana neman saurayi ruwa ajallo.

Budurwar wacce ta kware a fannin na’ura mai kwakwalwa, ta bayyana cewa baza ta iya girki ko wanki ba, saboda a koda yaushe aiki yayi mata yawa.

Inda ta bukaci shafin Twitter da ya samo mata saurayi daidai da ita.

Ta ce:

“Shekaruna 30 kuma ina neman saurayi. Ba zan iya girki ba, bazan iya wanki ba, aiki yayi mini yawa a koda yaushe. Twitter ki samo mini saurayi.

“Ni mace ce da ta riga ta san duk wani abu da namiji yake bukata.

“Kafin ma mu fara soyayya sai ka fara tabbatar mini da cewa ka cika namiji tukunna.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here