Hotuna: Matashi dan Najeriya ya kirkiri injin da yake mayar da kayan bola su zama man fetur

0
543

Wani matashi daga gabashin Najeriya mai suna Emeka Nelson, ya zama abin kwatance bayan ya samu damar kirkirar wani inji da yake mayar da leda da robobi su zama man fetur.

Matashin saurayin ya wallafa yawan abubuwan da wannan inji nasa yake iya yi a shafinsa na Facebook.

A rubutun nasa da ya wallafa a shafin matashin saurayin ya bayyana cewa injin yana mayar da kayan bolan irinsu roba da kuma leda da aka gama amfani dasu.

Ya kara da cewa injin na shi ka iya juya wadannan abubuwa su zama kalanzir, danyen mai, tiles, bulo da kuma kwanon rufi.

Nelson wanda ya sanyawa wannan inji nasa suna Mgbanwe C12, ya nuna godiyarsa ga mutanen da suka taimaka masa ya kammala hada wannan inji nasa. Ya ce wannan inji abin alfahari ne ga duka mutanen.

Ya ce: “Kowanne abu da yayi tasiri a rayuwa ana fara shi a hankali ne. Wannan shine Mgbanwe C12. Mun fara aikin mun kammala a cikin kwanaki uku da dare daya.

“Inji ne da yake mayar da kayan bola irinsu leda, roba da sauransu su zama man fetur, kalanzir, danyen mai, tiles, kwanon rufi, bulo da sauransu. Ina so nayi amfani da wannan dama na mika godiya ta ga kungiyar Emeka Nelson; wannan babbar nasara ce a garemu duka.”

The greatest things in life started from a little beginning.This is Mgbanwe C12a(an Improved design of C12).Designed…

Posted by Emeka Nelson on Wednesday, October 31, 2018

Press Lives ta kawo muku rahoton wani matashin dalibi dan Najeriya da ya samu nasarar kera keke napep mai amfani da hasken rana a cikin kwanaki 21 kacal.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here