Hotuna: Matar aure ta shirya auren dan gidan kishiyarta da ta raina tun yana dan shekara 7 a duniya

0
259

Mutane sun yi caa akan wata mata ‘yar kasar Rasha mai suna Marina Balmasheva, bayan ta bayyana shirin auren da take yi da yaron da ta raina tsawon shekara 10.

Matar mai shekaru 35 a duniya tayi suna matuka a kasar Rasha saboda bidiyon da take wallafawa na yadda ake rage kiba a kafafen sadarwa na yanar gizo, sai dai yanzu tana faman samun kalubale bayan ta shirya auren yaron da zamu iya kiranshi da danta dan shekara 20 mai suna Vladimir.

Ananova News ta ruwaito cewa dangantakar Marina da Vladimir ta karu ne a lokacin da take kokarin ganin ta rage kiba, inda ta rage kiba daga 132kg zuwa 58kg. Bayan sun gane cewa suna da soyayyar juna a cikin zuciyarsu, sai suka bayyanawa duniya ta sani.

Marina ta auri mahaifin Vladimir wanda yake da shekaru 45 na tsawon shekara 10, sai dai yanzu ta bayyana cewa ta kamu da soyayyar Vladimir. Bama wannan kawai ba, ta bayyana cewa sun gama shiri tsaf domin suyi aure su haifi yara tare.

Mutane basu caa a kanta ba har sai da ta wallafa hotonta dana Vladimir lokacin da yana shekara 7 ita kuma tana shekara 22 a duniya, inda kuma a daya gefen ta wallafa hotonsu a yanzu da suke soyayya.

“Ba zaka taba sanin yadda rayuwa za ta zame maka ba, kuma baza ka san lokacin da zaka hadu da wanda zai saka farin ciki ba,” cewar Marina a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Instagram. “Na san cewa wasu zasu yi ta zagina, amma muna cikin farin ciki ni da shi, kuma ina yi muku fatan samun farin ciki.”

Marina da tsohon mijinta Alesky sun dauki nauyin yara guda biyar tare, tare da ‘ya’yansa guda biyu da tsohuwar matarsa ta haifa masa. A wannan karon Marina na so ta haifi yaranta, inda wasu kafafen sadarwa na kasar Rasha sun bayyana cewa sun rabu da tsohon mijinta ne saboda bata haihuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here