Hotuna: Masoya sun angwance watanni 18 bayan haduwar su a Twitter

0
900

Wata budurwa ‘yar yankin Arewacin Najeriya ta wallafa hotunan bikinta a shafin Twitter, inda tayi bayanin yadda ta hadu angon nata a shafin na Twitter watanni 18 da suka wuce.

Da take bayyana lokacin da suka fara haduwa, budurwar mai suna @Aysha_yayari, ta ce angon nata ya fara yi mata magana a ranar wata Asabar da misalin karfe 7 na safe.

Ta ce:

“Kimanin watanni 18 da suka wuce, wannan mutumin kawai ya aiko mini da sako a shafin Twitter a ranar wata Asabar da misalin karfe 7 na safe (abin mamaki wanene yake yiwa budurwa magana a daidai irin wannan sanyin safiyar, kuma a karshen mako).

“Yanzu na auri wannan mutumin, kuma ina cikin farin ciki. Alhamdulillah.”

Amarya tare da Angonta cikin annushuwa | Photo Source: Twitter
Amarya tare da Angonta cikin annushuwa | Photo Source: Twitter

Amarya tare da Angonta cikin annushuwa | Photo Source: Twitter

To shi dama haka Allah yake lamarinsa, domin kuwa ance matar mutum kabarinsa, sai dai muce Allah ya basu zaman lafiya ya bayar da zuri’a dayyiba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here