Mujallar Forbes ta saki sunayen mutanen da suka fi kudi a shekarar 2020. A cikin jadawalin mutanen, Jeff Bezos ne na farko, inda yake da yawan kudi Dalar Amurka biliyan 113 ($113b).
Daga Jeff Bezos kuma sai Bill Gates wanda yazo a na biyu, da Dalar Amurka biliyan 98 ($98b). Sai Bernard Arnault, dake a kasar Faransa da yazo a matsayin na uku da Dalar Amurka biliyan 76 ($76b).
Warren Buffet da Larry Ellison sune suka zo na hudu dana biyar a cikin jadawalin. Shi kuwa fitaccen mai arzikin nan na nahiyar Afrika, wato Aliko Dangote, ya zo a matsayin na 162 a cikin jerin mutane 2,095 da suka fi kowa kudi a duniya, inda yake da Dalar Amurka biliyan 8.3 ($8.3b).
Mike Adenuga da Abdulsamad Isyaka Rabiu kuwa sun zo a matsayin 286 da 716, da yawan kudi Dalar Amurka biliyan 5.6 ($5.6b) da kuma Dalar Amurka biliyan 2.9 ($2.9b).
Ga dai jerin mutane bakwai din da suka fi kudi a duniya a kasa:
1. Jeff Bezos ($113bn)

Shekaru: 56
Kasa: Amurka
Kamfani: Amazon
2. Bill Gates ($98bn)

Shekaru: 64
Kasa: Amurka
Kamfani: Microsoft
3. Bernard Arnault ($76bn)

Shekaru: 71
Kasa: Faransa
Kamfani: LVMH
4. Warren Buffet ($67.5bn)

Shekaru: 89
Kasa: Amurka
Kamfani: Berkshire Hathaway
5. Larry Ellison ($59bn)

Shekaru: 75
Kasa: Amurka
Kamfani: Fasaha
6. Amancio Ortega ($55.1bn)

Shekaru: 84
Kasa: Spain
Kamfani: Zara
7. Mark Zuckerberg

Shekaru: 34
Kasa: Amurka
Kamfani: Facebook
Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:
Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa
Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa
YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com