Hotuna: Cikin otel din da Sarkin Thailand ya kulle kanshi a ciki da karuwai 20 saboda gudun Coronavirus

0
184

An ruwaito cewa Sarkin Thai, Maha Vajiralongkom, ya kulle kanshi a wani babban otel dake kasar Jamus tare da karuwai guda 20, bayan ya gudu daga kasar shi sanadiyyar cutar Coronavirus.

Sarkin mai shekaru 67 an ruwaito cewa ya dawo Otel din dake Sonnenbichi a yankin kudancin kasar Jamus, bayan ya dan kai ziyara ta kankanin lokaci kasar shi ta Thailand.

A rahoton da Bild ta ruwaito, Vajiralongkorn, da mutanenshi sun koma otel din inda suka kama sashe daya baki daya da ya kunshi wajen shakatawa da kayan alatu.

An ruwaito cewa karuwan nashi za su yi shiga irinta sojojin kamar dai yadda sojojin kasar Birtaniya suke yi.

Haka kuma an ware wani daki na daban da Sarkin zai dinga shiga yana sheke ayarsa da karuwan nashi.

Shafin otel din na yanar gizo ya nuna cewa babu daki kwata-kwata a otel din saboda Coronavirus, sai dai kuma wata ma’aikaciyar otel din ta bayyana cewa an hana su shiga sashen da Sarkin da mutanensa suka sauka.

Wani masani na kasar Thailand mai suna Adrew Macgregor Marshall ya sanar da Bild cewa, duka sashen otel din an yi masa ado da kayan kasar Thailand da kuma dukiya ta kasar Bangkok.

Karuwan sun mayar da wannan rayuwa da zasu yi tamkar caca, inda suke ganin duk wacce ta lashe gasar za ta samu arziki mai tarin yawa ita da danginta.

Wasu kuwa an tilasta musu ne suka bi Sarkin saboda suna tsoron abinda zai je ya dawo idan suka ki bin umarnin shi.

Kasar ta Thailand dai an kulleta an hana zirga-zirga tun a watan Maris, inda mutane 2,992 suka kamu da cutar ta Coronavirus, sannan kuma mutum 55 suka mutu sanadiyyar cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here