Hotuna: Budurwa tayi amfani da kwarewarta a kwalliya ta canjawa kanta kama zuwa ta shugaba Buhari

0
853

Wata budurwa da ta kware wajen iya kwalliya mai suna Richard Jane, ta nuna kwarewarta wajen iya kwalliya, inda ta wallafa yadda ta canja kamarta zuwa kamar shugaba Buhari.

Ta roki mabiyanta da suyi sharhi akan hoton, inda take ganin cewa tayi kokari sosai wajen wannan kwalliya.

Mutane da dama sunyi ta magana akan wannan hoto na Jane, inda suka dinga jinjina mata.

Ga dai hotunan na ta a kasa:

Today’s episode on how bored are you, lolDid an imitation makeup of Buhari Close enough I guess🙃Show some love🙏

Posted by Richard Jane on Thursday, June 25, 2020

Haka kuma Press Lives ta kawo muku labarin wata mata mai shekaru 33 da ta girma a Budalangi, mai suna Tina Akello, wacce take da burin zama soja tun tana yarinya.

Bata taba tunanin za tayi aiki a kusa da gawa ba, amma komai ya canja a lokacin da aminiyarta ta mutu a shekarar 2016.

Tina wacce ta koma Mombasa a shekarar 1999, tana daya daga cikin dubunnan mutanen kasar Kenya da kasuwancinsu ya durkushe saboda cutar coronavirus da ta shafi ko ina a duniya.

Sanadiyyar annobar, iya ma’aikatan lafiya kawai aka amincewa su kusanci gawar mutane, wadanda ake gaggawar binne su da sun mutu kamar yadda sharuddan ma’aikatar lafiya ta gindaya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here