Hotuna: Budurwa mai tallar gyada da aka yiwa fyade ta haifi ‘yan uku

0
623

Budurwa ‘yar shekara 20 da take tallar gyada ta fara yawo a shafukan sadarwa, bayan ta haifi ‘yan uku sakamakon fyaden da aka yi mata.

Labarin da wata mai amfani da shafin Facebook ta wallafa mai suna, Precious Oluomachi Livingstone, ta bayyana cewa budurwar mai tallar gyadar ta dauki cikin jariran ne bayan anyi mata fyade a lokacin da take tallar gyadar.

Daukar cikin ta hanyar fyade ba shine abin da budurwar take magana a kai ba, abin da take magana a kai shine yadda budurwar ta bar cikin har Allah ya sanya albarkar samun jarirai uku.

A daidai lokacin da muke rubuta wannan rahoto dai babu wani cikakken bayani game da budurwar da kuma ‘ya’yan nata. Za mu sanar da masu bibiyar mu da zarar mun gano hakan.

Ga dai abinda budurwar ta wallafa da kuma hotunan su a kasa:

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here