Hotuna: Asirin Malamin makaranta da ya aikawa dalibarshi sakon WhatsApp akan yana so yayi zina da ita ya tonu

0
126

Wani mutumi ya zargi Malamin makaranta da aikawa dalibarshi mai shekaru 15 a duniya sakon WhatsApp, inda ya nemi yayi lalata da ita.

Mutumin mai amfani da shafin sadarwa na Instagram mai suna @jay.mzz, ya wallafa hotunan hirar malamin da ya dinga aikawa dalibar mai karancin shekaru, inda ya dinga tambayarta akan yana so yayi zina da ita bayan an koma makaranta.

Abubuwan dake cikin hirar tasu yayi muni da yawa, inda har akwai hotuna dake nuni da mace da namiji na saduwa.

Dalibar ta nuna cewa bata ji dadin irin abinda malamin yake turo mata ba, amma yaki dainawa inda ya cigaba da aika mata da irin wannan maganganu a kokarinshi na shawo kanta ta yadda da abinda yake so.

Da dalibar ta nuna masa cewa ya girme ta sosai, sai yace mata tazarar dake tsakaninsu ba wani yawa ne da ita ba.

Da yake wallafa hotunan hirar malamin da dalibar, mutumin ya bayyana cewa: “Wannan ita ce hirar daliba ‘yar SS2 mai shekaru 15 a duniya da malaminta. Wannan kwata-kwata bai kamata ba, kuma mutum irin wannan bai kamata yayi aiki a wajen da akwai yara ba.

“Duk wanda ya san inda wannan mutumin yake ya taimaka ya kai rahoto ga makarantar da yake aiki, kafin wani abu mummuna ya faru da wannan daliban.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here