Hotuna: An gina otel din zinare na farko a duniya a kasar Vietnam

0
1673

Otel na farko a duniya da aka gina shi da zinare ya fara aiki a kasar Vietnam.

Otel din wanda yake da hawa 24, an sanya komai a ciki na zinare, hatta abubuwan ciki, irinsu cokali, kofi, kayan bandaki da kujeru duka na zinare ne, an kashe dala miliyan dari biyu ($200m), kimanin naira biliyan 78 a kudin Najeriya, sannan kuma an shafe shekaru 11 ana gina otel din.

Hatta ruwan shayi ana sanyawa mutane a cikin kofin zinare ne, haka kuma an gina gidan wanka na zinare.

Otel din da aka sanya masa suna ‘Dolce Hanoi Golden Lake Hotel’ yana cikin babban birnin kasar na Hanoi, kusa da wani karamin kogi, otel din yana da dakuna dari hudu.

Ana biyan dala dari biyu da hamsin ($250), kimanin naira dubu casa’in da bakwai (N97,000) a kowanne kwana daya a cikin otel din, sannan kuma akwai bangaren da mutane ka iya karbar haya na shekaru da yawa idan suna so.

Wani mai suna Phillip Park, wanda ya fito daga yankin Koriya ta Kudu, ya ce:

“Lokacin dana zo naji kai na tamkar wani sarki ne.”

Nguyen Huu Duong, shugaban kungiyar Hoa Binh, kungiyar da ta mallaki otel din ya ce:

“Muna son talaka da mai kudi kowa ya zo ya kama daki. Kungiyar mu tana da kamfanin da zai iya gina abubuwa na zinare, saboda haka kudin kayayyakin mu a nan babu wani tsada.”

A yayin da annobar coronavirus ta hana zirga-zirga tsakanin kasashe, Duong yayi rokon samun hanyar da zai samu ya mayar da kudin da suka gina otel din a shekarar 2021.

Ga dai wasu daga cikin hotunan otel din a kasa:

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here