Kasar Saudiyya ta bude asibitin rakuma wanda yafi kowanne girma a duniya a yankin Qassim. Yana daya daga cikin asibitoci mafi girma a duniya, inda aka kashe kimanin dala miliyan 26.7, kawai domin kula da rakuma.

Asibitin wanda aka sanyawa suna Salam Veterinary Group Camel Hospital, gwamnan yankin Qassim, Yarima Dr. Faisal bin Mishaal bin Saud bin Abdul’aziz ne ya bude.

A rahoton da kungiyar abinci da harkokin gona ta fitar, yankin Larabawa na da yawan rakuma guda miliyan 1.6. Kuma kimanin kashi 53 cikin 100 suna cikin kasar Saudiyya ne, yayin da yawan rakuman dake cikin Hadaddiyar Daular Larabawa 30,000 ne kawai.

Akwai wasu asibitoci irin wannan da yawa da aka gina su a yankunan Qatar da Dubai.

A shekarar 2015, Qatar ta bude irin wannan asibitin. Bayan wannan an bude wani asibitin rakuma mai suna Dubai Camel Hospital (DCH), inda aka kashe dala miliyan 10 a shekarar 2017, wanda shine babban asibiti na biyu da aka ginawa rakuma.

A shekarar 2019 Dubai Camel Hospital (DCH), ya kara kaimi da kashi 50, inda yake yiwa rakuma 30 magani a lokaci daya, kamar yadda dai gidan talabijin na Emirates 24/7 ya ruwaito.

Nawa ne farashin rakumi?

A rahoton da New York Times ta fitar, farashin rakumi na tashi daga dala 2,700 zuwa dala 815,000.

Dawakai mata wato ‘Godiya’ sun fi rakuma daraja a kasuwa, kamar yadda CNN ta ruwaito cewa, Yariman Dubai mai jiran gado, Sheikh Hamdan bin Mohammed ya sayi godiya saboda tsananin kyawunta akan kudi dala miliyan 2.7.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here