Home Blog

Irin tashin hankalin dana shiga bayan na kamu da Coronavirus na kuma gogawa ‘yata – Rahma Abdullahi

Sakatariyar majalisar karamar hukumar Abuja, Rahma Abdullahi, ta bayyana cewa ta kamu da cutar coronavirus a wajen aiki, kuma ta gogawa ‘yarta.

Ta ce ta shiga tashin hankali da ciwo wanda ba za ta iya misaltawa ba.

Sai dai cikin ikon Allah duka ‘ya da uwar sun samu lafiya duka sun dawo gida lafiya lau.

Ta ce: “Na dauki cutar COVID-19 a kokarin da nake na yin aiki, kuma na gogawa diyata. Ciwon da tashin hankalin dana shiga ba zai iya misaltuwa ba. Yau ni da diyata abar kaunata mun dawo gida lafiya lau. Nagode Allah, kuma nagode muku da soyayyarku da kuma addu’o’inku. Mun fi karfin coronavirus.”

Yayin da wani mai suna @Horlufemi yayi mata sharhi da cewa zazzabin cizon sauro ne ya kamata. Sannan ya tambayeta akan nawa aka biya ta hado wannan karya. Rahama ta ce yanzu babban abinda take buri shine tayi kokarin wayar da kawunan miliyoyin ‘yan Najeriya akan yaduwar cutar. Inda ta ce cutar gaskiya ce ba karya ba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

Tashin hankali: Wata mata ta zubawa yarinyar da aka bata riko ruwan zafi da barkono a gabanta

Wani rahoto da jaridar Tribune Online ta ruwaito, ya nuna yadda wata mata dake zaune a yankin Iyara cikin garin Warri dake jihar Delta ta batawa wata ‘yar uwarta gaba.

Matar wacce ta aikata laifin a ranar Alhamis ta zubawa ‘yar uwartan wacce take zaune da ita ruwan zafi da barkono a gaba akan zargin da take na cewa yarinyar tayi lalata da wani.

Dalilin haka ya sanya mutanen yankin suka kama matar wacce aka boye sunanta zuwa sakatariyar matasa, inda aka umarceta akan ta kai yarinyar asibiti wacce take ta ihun kuka sakamakon zafi da radadi dake damunta a gabanta.

Daga baya kuma an ruwaito cewa ba a kai wannan lamari hannun ‘yan sanda ba, saboda a yanayin dokar wannan yanki lamari irin wannan ana shawo kanshi a tsakanin al’ummar yankin ne.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

Ina so na zama fitaccen mawaki idan na mutu na shiga Aljannah – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce yana so ya shiga Aljannah ko dan ya shiga cikin kungiyar mawakan Aljannah.

Obasanjo ya bayyana haka a lokacin da yaji wata waka da aka yi a cocin Apostolic Faith Church dake Igbesa, jihar Ogun. Obasanjo ya yiwa Kiristoci gargadi a Najeriya da su shirya zuwan Isa Al-Masihu a karshen duniya.

“Ya kamata ku shirya sosai domin ubangiji yana nan dawowa. Ina da aboki da yace idan muka mutu muka shiga Aljannah sai mun gaji da yiwa ubangiji waka, kuma Aljannah za ta zama kamar gidan yari babu dadin zama.

“Amma ni abinda na gani a mahangata shine, zan shiga Aljannah, zan kuma shiga cikin kungiyar mawaka. Idan har wannan shine misalin yadda ake yabon ubangiji a Aljannah, to zan so shiga wannan kungiya. Idan har abinda na gani a nan shine misali na yadda Aljannah take to zan so shiga Aljannah.

“Isah Al-Masihu ya zo duniya ne domin ya nuna mana hanyar rayuwa ya kuma ceto mu daga halaka.

“Allah zai iya gyara Najeriya, amma dole sai mun kira shi ya shigo cikin rayuwar mu tukunna. Abinda zamu yi a kasar nan na hannun mu.” Ya ce.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

Hotunan wata gawa da aka yi mata ado aka dinga daukar hotuna da ita ya jawo kace-nace a shafukan sadarwa

Hotunan wani mutumi da ya mutu da aka dandasa masa kwalliya ‘yan dangi kowa da kowa yazo ake daukar hoto da shi yana ta faman yaduwa a shafukan sadarwa, inda mutane ke ta cece-kuce a kanshi.

A yadda rahoto ya nuna, mataccen mutumin yana ajiye a dakin ajiye gawa na asibiti fiye da watanni hudu inda aka yi masa ado sosai, dangin shi suke zuwa suna daukar hotuna da shi a yayin da aka tada shi tsaye.

Mamacin a yadda rahotanni suka bayyana sunansa Dr Luke Nkanele, wanda yake daya daga cikin manyan dakarun St Mulumba.

Har yanzu dai ba a tabbatar a wace kasa ne aka dauki wannan hotuna ba a daidai lokacin da aka wallafa rahoton.

Sai dai hotunan sun sanya mutane suna ta kace-nace a shafukan sadarwa.

Ga dai hotunan a kasa:

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

Duka masifun da ake samu a duniya na da nasaba da cin nama da kifi da mutane ke yi – Malamin Addini

Babban faston cocin International Missionary Crusade Fellowship, Archibishop David Irefin ya ce duka tashin hankalin da ake samu a duniya na da nasaba da cin nama da kifi da mutane ke yi.

Irefun ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar Leadership tayi da shi. A cewar shi, ubangiji bai bawa mutane umarnin kashewa da cin dabbobi ba. Ya ce idan har mutane na son zaman lafiya a duniyar nan to dole kowa ya daina cin nama da kifi a koma cin gayayyaki.

“Cin ganyayyaki daga wajen ubangiji ne. Ya ce babu wani waje da ubangiji ya ce mutane su ci kifi ko nama. Haka kuma duk masu biyayya gare shi zasu bi umarnin shi. ‘Duka masifun da ake fama da su a duniya sun samo asali da cin nama da kifi ne.”

“Kin bin umarnin abinda ubangiji ya ce zai saka mutane cigaba da zama cikin tashin hankali da suka hada da cututtuka, annoba, da mace-amce.” Irefun ya ce yafi mutane su rungumi abinda ubangiji yace kowa ya zauna lafiya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

Yadda matata da aure da komai ta gudu wajen tsohon saurayinta take kwanciya da shi – Miji ya koka

Wani mutumi dan kasar Afrika ta Kudu ya hau shafinsa na Twitter, inda yake bayyana labarin shi mai ban tausayi akan yadda ya rabu da matarsa da suka yi aure tsawon shekara biyu.

Mutumin mai suna @DMlamla, ya ce shi da tsohuwar matar tashi sunyi soyayya tsawon shekaru bakwai, kuma sunyi aure tsawon shekara biyu, sai ya fara ganin canji a wajenta a lokacin da ta samu aiki. Daga baya ya gano cewa tana zuwa wajen tsohon saurayinta. Kokarin da yayi wajen jawo hankalinta gare shi ya tafi a banza, saboda ta sanar da shi cewa har yanzu tana son tsohon saurayin nata, kuma shine dama wanda take so tun asali.

Ga dai abinda ya ce:

“Labarin rabuwa ta da matata. Mun yi shekara 7 muna soyayya, sannan muka yi aure na tsawon shekara biyu. Ta samu aiki, kawai sai na fara ganin canji a wajenta.

“Na kamata sama da sau uku ita da tsohon saurayinta, amma ta cigaba da cewa sun rabu, nayi kokarin daidaita abubuwa tsakanina da ita, amma abu bai yiwu ba. Na kira iyayena suma basu samu damar shawo kanta ba.

“Daga baya ta sanar dani cewa zai yi wuya ta iya rabuwa da shi saboda tana matukar son shi. Dalilinta shine tayi aure da wuri, kuma suna matukar son junansu da tsohon saurayinta hakan ya sanya baza su iya rabuwa ba.

“Hankalina ya tashi sosai, wannan shine karo na farko dana fara yiwa mace kuka a rayuwata, bazan manta yadda na durkusa ina rokonta akan ta yi hakuri ba.

‘Abinda ya sanya na yanke shawarar rabuwa da ita shine, lokacin da ta gaya mini cewa dama can tsohon saurayinta shine mijin da take mafarki, kawai ni dai ta san mutum ne mai kirki, amma zaman da take yi dani kawai zama ne take yi na hakuri.

‘Kawai dai abinda na sani shine baza ka taba yin daidai ga mutumin da ba naka ba.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

Yadda mazaunanta suke rawa ne ya bani sha’awa nayi mata fyade – Cewar Sani Garba da ya yiwa ‘yar shekara 60 fyade

An gabatar da wani mutumi dan shekaru 32, mai suna Sani Garba, a helkwatar ‘yan sanda ta jihar Neja da laifin yiwa wata tsohuwa ‘yar shekara 60 fyade.

Sani dai ya nemi ayi masa afuwa bayan ya bayyanacewa yanayin yadda yaga mazaunan tsohuwar suna rawa ne ya bashi sha’awa, shiyasa ya afka mata.

A ranar Juma’a ne jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa jami’in ‘yan sanda dake ofishin Suleja ne suka kaama shi, inda ya kara da cewa za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.

An gano cewa mutumin ya shiga gidan matar a ranar 18 ga watan Yuli, 2020, da misalin karfe 4:30 na yamma yayi mata fyade.

Garba ya bayyanawa manema labarai cewa, mutumin ya yiwa tsofaffi guda uku fyade a wannan yanki.

Ya ce: “Tunda bani da kudin da zai iya daukar nauyin budurwa, na yanke shawarar yiwa tsofaffi fyade a yankina, kuma ina jin dadin yin hakan. A lokuta da yawa ina tambayar kaina mai yasa nake yin wannan abu marar dadin ji?”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

Yadda Sheikh Muhammad Nuru Khalid ya farantawa ‘yan Kannywood rai

Ba tun yau ba ake samun takun saka tsakanin jaruman Kannywood da Malaman addini ba, inda hakan yake jawo maganganu masu yawa ga jaruman, domin kuwa akasarin al’umma na goyon bayan Malaman dake caccakar ‘yan fim din, wadanda ake zargin su da bata tarbiyya da sunan fadakarwa.

Wannan matsala duk da dai cewa ba jarumi daya ta shafa ba, amma jarumai irin su Adam A Zango, Ali Nuhu, Ado Gwanja sun fi samun suka ta kai tsaye daga Malaman sai kuma wasu ‘yan tsiraru daga cikin mata irin su Rahama Sadau da sauransu.

Sai dai bayyanar wata lakca ta fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid ta sanya jaruman jin dadi, inda suka ga cewa ba duka Malaman ne suke yi musu kallon bata gari ba, inda suka dinga wallafa tsakuren lakcar, inda jarumai irinsu Ali Nuhu, Saifullahi Safzor, Ali Gumzak, Nasir Gwangwazo da sauransu suka wallafa.

Ga dai bayanin Malamin, wanda ya sanya jaruman dariya:

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

Abin sha’awa: Yadda wata tsaleliyar budurwar ta auri wani saurayi jim kadan bayan haduwar su a Twitter

Yayin da aure yake wahala a wannan zamani, musamman wannan lokaci da mata suke neman ninka maza a yawa. Hakan bai hana wasu da yawa samun abokanan aure ba, musamman wadanda basu dauki rayuwar da zafi ba.

Duk da dai kowa yasan cewa aure lokaci ne na Allah dabarar mutum baza ta saka yayi ba, amma da yawa suna dorawa kansu karya da son abin duniya da ya sanya auren baya yiwuwa.

Wata tsaleliyar budurwa da ta wallafa hotunanta da wani saurayi a shafinta na Twitter ta bayyana yadda soyayyarsu ta samo asali har ya zuwa auren da suka yi.

Budurwar mai suna Ummeeta Rabiu, wacce alamu ke nuni da cewa sun shekara da aure, ta wallafa hotunan a shafinta inda ta ce: “Har yanzu ina mamaki haduwa a Twitter ne ya kawo mu wannan matsayi. Dama na sha fada cewa mu gwada mu gani. Da yanzu ba zan same ka ba. Ina matukar godiya ga Allah da irin rayuwar da muke yi tare. Alhamdulillah, ina sonka yanzu da har abada.”

Wannan rubutu da Ummeeta ta wallafa ya bawa mutane da dama sha’awa, inda wasu suke cewa irin wannan kyakkyawar budurwa bata nuna girman kai ba wajen yiwa saurayi magana a shafukan sadarwa, amma sai kaga wata can da ba kyau ne da ita ba ta dauki girman kan duniya ta dorawa kanta.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

Tsananin kishi ya sanya wani saurayi kashe kanshi a Kano saboda wani ya kwace mishi budurwa

Wani saurayi dan shekara 25 da aka bayyana sunanshi da Ashiru Musa Danrimi ya cakawa kanshi wuka da tayi sanadiyyar mutuwar shi a Kano, bayan budurwar shi ta ce bata son shi taje ta auri wani.

A yadda rahotani suka nuna, wanda yake zaune a Kadawa dake cikin karamar hukumar Ungogo, ranshi ya baci bayan budurwar shi mai suna Ummi Muhammad, ta yanke hukuncin auren wani, bayan ya gama yi mata wahala ta kudi a lokacin da suke soyayya. Hakan ya sanya ya dauki wuka ya cakawa kanshi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ‘yan sanda sun yi gaggawar garzayawa da saurayin zuwa asibitin Murtala, inda aka tabbatar da cewa ya mutu. Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Habu Sani, ya bayar da umarnin gabatar da bincike akan wannan lamari.

Makotan mutumin sun kadu a lokacin da suka ji wannan labari na mutuwar shi, saboda da yawa daga cikinsu da suka san suna soyayya basu taba tunanin soyayyar za ta kare a haka ba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

Sara Haba: Mace ta farko a duniya da ta fara zuwa Makkah a keke

Wata mata ‘yar kasar Tunisia, mai suna Sara Haba, ta bar tarihi a duniya, bayan tayi amfani da keke taje kasar Saudiyya.

Ta kammala tafiyarta a cikin kwanaki 53. Ta dinga sanya hotunanta a lokacin da take wannan tafiya, hakan ya sanya tayi suna sosai. Ta bi ta cikin Saharar Sudan daga nan ta shiga ta Egypt.

Ta bayyana a shafinta na Instagram cewa taji tsoro sosai a lokacin da ta fara wannan tafiya. Saboda bata da tabbacin za ta iya jure wannan tafiya da ta shafe shekaru tana mafarkin yi.

Saboda ita daya ce ta ce, wani lokacin ta kanji kamar ta hakura da tafiyar. Sai dai hakan ba sanya ta ja da baya ba, ta cigaba da kokarin ganin ta cika wannan buri na ta.

Jarumar macen, ta isa birnin Makkah, kuma akan hanyarta tayi ta haduwa da mutane da suka dinga yi mata addu’ar samun sa’a. Haka kuma ta karbi sakonni na addu’a da yawa daga wajen mutane domin tayi musu addu’a a kasa mai tsarki.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

A karon farko an gabatar da Sallar Juma’a a Haghia Sophia bayan shekara 86

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya shiga cikin daruruwan al’ummar Musulmai inda suka gabatar da Sallar Juma’a a Masallacin Hagia Sophia wanda aka dawo da martabar shi kwanakin baya.

An gabatar da kiran Sallah a Masallacin na Hagia Sophia a ranar ta Juma’a, inda ta zama sallar juma’a ta farko da aka gabatar a Masallacin bayan shekara 86 da wajen ya kwashe a matsayin wajen ajiye kayan tarihi.

A ranar 10 ga watan Yuli ne, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya mayar da wajen Masallaci.

Daga yanzu dai wannaan wuri za a cigaba da bude shi ga Musulmai da suke da bukatar yin sallolinsu a ciki, dama wadanda basu Sallah za a basu damar shiga.

Wannan dai labari ne mai dadi ga al’ummar Musulmai yayin da za a cigaba da amfani da wannan dadadden wuri na tarihi a matsayin Masallaci. Bayan haka kuma Musulmai na ko ina a fadin duniya suna ta yabawa shugaban kasar ta Turkiya akan wannan mataki da ya dauka.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

Irin tashin hankalin dana shiga bayan na kamu da Coronavirus na...

0
Sakatariyar majalisar karamar hukumar Abuja, Rahma Abdullahi, ta bayyana cewa ta kamu da cutar coronavirus a wajen aiki, kuma ta gogawa 'yarta...
error: Content is protected !!