Bayan sanar da ranar da za a binne tsohon gwamnan jihar Oyo da iyalanshi suka yi, kan cewar za a binne shi a ranar Lahadi 28 ga watan Yuni, a cikin Masallaci, Musulman Najeriya sun nuna rashin jin dadinsu akan hakan.
Legit.ng ta ruwaito cewa mai taimakawa marigayin, Bolaji Tunji, ya ce tsohon maigidan nashi za a binne shi a cikin Masallacin Sanata Ishaq Abiola Ajimobi, dake Oke-Ado, a garin Ibadan da misalin 12 na rana.
Ya ce bayanin binne shi din ya biyo bayan tattaunawa da iyalin marigayin suka yi da gwamnatin jihar Oyo da ta Legas.
A wani rahoto da wakilin Legit.ng, Ibrahim Akinola, ya ruwaito cewa wasu Musulmai ‘yan Najeriya sun yi caa akan iyalan Ajimobi akan maganar binne tsohon gwamnan a cikin Masallaci, inda suka ce yin hakan zai saka dole a daina amfani da Masallacin.
A yayin da yake martani akan wannan lamari, babban Malamin Musulunci, Ustadh Ibrahim Tijjani, ya ce Annabi Muhammad (SAW), ya haramtawa Musulmai binne mutane a cikin Masallaci, sannan kuma ya hana gina Masallaci akan kabari, haka kuma ya kara da cewa Annabi Muhammad (SAW) ya tsinewa duk wadanda suka binne mamaci a cikin Masallaci.
Ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya haramta binne mamata a cikin Masallaci da kuma gina Masallaci a kansu; haka kuma ya tsinewa duk wanda yayi haka. Ya gargadi mutanen shi a lokacin da yake gabannin komawa ga Allah.”
“Annabi (SAW) ya ce wannan al’adar Yahudu da Nasara ce, kuma hanya ce da za ta kai mutum ga hada Allah da wani. Gina Masallaci akan kabari da kuma binne mamata a cikin Masallaci na kai mutane ga hada wadannan mamata da Allah.
Ya ce Allah ya ce: “Masallaci daki ne na Allah ne shi kadai, saboda haka kada ku hada kowa da Allah.” (Suratul Jinn 72:18).
Haka wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Sheikh Abdullahi Qassim, yayi gargadi akan binne Ajimobi a cikin Masallaci.
Ya ce: “Musulmai mutanen jihar Oyo ya kamata ku tashi tsaye, ku taimaka kada ku binne Sanata Ajimobi a cikin Masallacin nan. Kada ku hana Musulmai zuwa Masallacin.”
Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:
Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa
Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa
YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com