Gwamnonin Arewa sun cimma matsaya wajen kawo karshen Almajiranci a yankin Arewa baki daya – El-Rufai

0
130

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana sanarwar kawo karshen karatun allo da almajiranci a jihar Kaduna, inda ya kara da cewa kuma yawancin gwamnonin yankin sun dauki wannan mataki a jihohinsu.

A wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels TV El-Rufa’i, ya bayyana cewa tuni sunyi nisa wajen gabatar da nazari akan dokoki wajen sauya tsarin ta inda zai zama tsarin almajiranci ba zai kara tasiri a jihar ta Kaduna ba.

Gwamnan ya kara da cewa a halin da ake ciki yanzu, gwamnatin jihar Kaduna ta samu nasarar mayar da almajirai sama da dubu talatin (30,000) zuwa jihohin da suka fito.

A kwanakin baya gwamnonin jihohin arewa sunyi ta mayar da almajirai zuwa ainahin jihohi da garuruwansu na haihuwa, inda zuwan cutar Coronavirus ya sanya lamarin ya kara kamari.

Da yawa daga cikin gwamnonin sun kara karfafa shirin mayar da almajiran jihohinsu bayan bayyanar cutar, inda ake ganin hakan zai kawo karshen matakin magance matsalar barace-barace da yara kanana suke yi a wasu jihohi na kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here