Gwamnatin tarayya za ta sallami ma’aikatan N-Power 500,000 a cikin watan nan

0
612

Ministar jinkai da cigaban jama’a Sadiya Umar Farouq ta ce ma’aikatan N-Power na rukunin A da rukunin B za su kammala aikinsu a ranar 30 ga watan Yuni da kuma 31 ga watan Yuli.

Shirin dai ya dauki ma’aikata 500,000, inda aka fara daukan mutum 200,000 a rukunin farko, wanda suka fara aiki a watan Satumbar shekarar 2016, sannan kuma aka dauki rukuni na biyu na mutum 300,000, da suka fara aiki a watan Agustan shekarar 2018.

A ka’ida ma’aikatan za su yi shekara biyu ne kawai suna aiki, amma rukunin farko da aka fara dauka a yanzu haka sun cinye sama da watanni 40.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce gwamnatin tarayya ta fara sauya tsarin rukunan guda biyu zuwa tsarin kasuwanci na gwamnati.

“Mun fara canja tsarin ma’aikatan rukunin farko dana biyu zuwa tsarin kasuwanci, sannan zamu sanya ma’aikatu na ‘yan kasuwa su dauki wasu daga cikinsu, bayan kammala gwada kwarewar su a fannoni daban-daban.

“Gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen cigaba da fadada tsarin, saboda haka ne ma yanzu take shirin daukar wasu ma’aikatan na N-Power.

“Bisa la’akari da haka, ma’aikatar ta sanar da dakatar da rukunin farko a ranar 30 ga watan Yuni, 2020, sannan rukuni na biyu za a dakatar su a tsarin a ranar 31 ga watan Yuli, 2020.”

Ma’aikatar za ta fara daukar sababbin ma’aikata a tsarin daga ranar 26 ga watan Yuli, 2020.

Za a bude shafin yanar gizo domin mutane suyi rijista a ranar 26 ga watan Yuni.

Shirin na N-Power din dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kawo shi a shekarar 2016, a kokarin da yake na rage rashin aikin yi a cikin al’umma da kuma rage talauci tsakanin jama’a.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here