Gwamnatin tarayya za ta ragewa ma’aikatan N-Power wa’adin yin aiki

0
1431

Daga yanzu ma’aikatan N-Power za su dinga yin aiki kasa da shekara biyu, cewar ministar jin kai da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouq.

Ta ce wannan wani bangare ne na sake fasalin tsarin da gwamnati za ta yi don ganin shirin na N-Power ya inganta, cewar ministar a wata zantawa da tayi a Abuja.

Ta ce ma’aikatar tayi nazari akan tsarin don karfafa shirin da kuma tafiyar da shi yadda ya dace.

“Daga cikin sake fasalin za a rage wa’adin shekarun da suke yi, da kuma kaddamar da sabon tsarin da zai taimaka wajen canja shirin N-SIP da zai taimakawa marasa karfi, ta hanyar samar da damar yin amfani da abubuwa na cigaba, koyar da sana’o’i, da dai sauransu domin fito da al’umma daga kuncin talauci,” ta ce.

Bayan haka kuma, ta ce, za a yiwa mata rijista a cikin shirin don karfafa musu guiwa ta yadda za su iya samun kudin harkokin rayuwa wadatacce.

Haka kuma sanarwar ta ce za a mai da hankali wajen juya ilimi a koyar da sana’ao’i ga al’umma ta hanyar samar da dama a gare su don yi kasuwanci a zamanance.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here