Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda za ta dauki ma’aikata 774,000 a fadin Najeriya

0
777

Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda za ta dauki ma’aikata 1,000 a cikin kowacce karamar hukuma daga cikin kananan hukumomi 774 na fadin Najeriya.

Karamin ministan ma’aikata na Najeriya, Festus Keyamo, shine ya bayyana haka a jiya Alhamis, 28 ga watan Mayu, ga manema labarai inda ya ce za a fara daukar ma’aikatan a ranar 1 ga watan Oktoba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta kafa kwamiti a kowacce jiha da za ta dauki wadannan mutane a cikin kowacce karamar hukuma.

A cewar Keyamo, wannan kwamiti ta musamman da za a kafa ita ce za ta kawo sunayen ma’aikatan kowacce karamar hukuma dake jihohin.

Ministan ya bayyana cewa za’a bude shafi na yanar gizo inda za a sanya sunayen ma’aikatan da aka zaba kowa zai shiga ya ga sunansa.

Keyamo ya ce za’a biya kowanne ma’aikaci naira dubu ashirin (N20,000) a kowanne wata.

A wani rahoton kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisa ta bashi damar karbo bashin dala biliyan biyar $5.5b, don samun damar kammala wasu aiki masu muhimmanci da aka fara a wannan shekara ta 2020.

Sanarwar wannan ciyo bashi dai na kunshe a cikin wata takarda da fadar shugaban kasar ta aikawa ‘yan majalisar wakilai na tarayya a jiya Alhamis 28 ga watan Mayu, 2020.

A cewar shugaban kasar gwamnati za ta yi amfani da kudin wajen kammala manyan ayyukan gwamnatin tarayya, sannan kuma za tayi amfani da wani sashe na kudin wajen cigaba da yaki da cutar COVID-19.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here