Gwamnatin tarayya ta bayyana mutanen da suke yada cutar COVID-19 cikin al’umma

0
302

Cibiyar lura da manyan cututtuka ta Najeriya (NCDC), ta bayyana cewa ‘yan Najeriya dake tsakanin shekara 20 zuwa 40 sune suke yada cutar COVID-19 a cikin al’umma.

Darakta Janar na cibiyar, Chikwe Ihekweazu, shine ya bayyana haka a lokacin wani taro da aka gabatar a jiya Alhamis, 2 ga watan Yuli, The Cable ta ruwaito.

Ya ce duk da dai matasa ne suke yada cutar, amma dattijai da suke da sama da shekaru 50 su ne suka fi mutuwa.

Shugaban cibiyar ta NCDC ya bayyana cewa kowa ya sani dai cewa matasa ne suke yada cutar ta COVID-19 a Najeriya.

“Kamar yadda mutane suke ta kara kamuwa da cutar a fadin duniya. Alamu sun nuna cewa matasa ne suka fi yada cutar, ba wai yara ba, mutane da suke tsakanin shekara 20 zuwa 40, sune suke yada cutar tsakanin al’umma. Amma kuma wadanda cutar tafi kashewa sune ‘yan shekara 50 zuwa sama,” ya ce.

Ya bayyana cewa mutum 3 cikin 5 na mutanen da suka mutu sakamakon COVID-19 duka tsofaffi ne da suke da shekaru 50 zuwa sama.

Ihekweazu ya ce akwai bukatar a kare tsofaffi daga kamuwa da cutar a fadin Najeriya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here