Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, yana shan yabo daga wajen ‘yan Afrika a shafukan sada zumunta, bayan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta bawa al’ummar kasar baki daya wuta da ruwa kyauta na watan Afrilu, Mayu da Yuni.

Sai dai kuma a wata sabuwar sanarwa da ya sake fitarwa, shugaban kasar ya sake kara watannin, inda ya ce za a sake bawa al’ummar kasar ruwa da wutan na tsawon wasu wannin guda uku saboda annobar coronavirus da ta addabi al’ummar duniya.

A lokacin da yake bayani ga al’ummar kasar shugaban kasar ya ce babu wani dan kasar Ghana da za a yankewa wutar lantarki ko ruwan sha daga yanzu zuwa watanni uku masu zuwa.

“Kamfanin wuta da ruwa na kasar Ghana mun basu umarnin bawa al’ummar kasa isasshiyar wutar lantarki a wannan lokaci. Babu wanda za a yankewa wuta ko ruwa a fadin kasar nan.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here