Gwamnatin kasar China na hana Musulmai mazauna Uighar haihuwa

0
587

Wani rahoto da wani dan kasar Jamus mai suna Adrian Zenz, ya jawo bukatar bincike akan tauye hakkin dan adam da hukumomin kasar China suke yi.

Kasar ta China na tauye hakkin matan Musulmai dake zaune a Uighar dake Xinjiang. Rahoton wanda Adrian Zenz, daya daga cikin manyan masana na duniya akan manufofin gwamnatin kasar China kan al’ummarta.

Binciken dai an gabatar da shine akan takardu na dokoki da kuma hira da wasu mata mazauna yankin.

“Sakamakon rikice-rikicen da ya samo asali a cikin shekarar 2016, ya mayar da Xinjiang ta zama jihar ‘yan sanda baki daya,” cewar Zenz a gabatarwar da yayi game da rahoton nasa.

“Yayin da doka akan yanayin yadda mutane za su haihu ta jima tana aiki a kasar ta China, lamarin a Xinjiang yayi tsamari sosai, musamman ma bayan gabatar da kudurin a farkon shekarar 2017 da wasu daga cikin jami’an kasar ta China suka gabatar.

Binciken Zenz ya gano cewa yawan mutane a Xinjiang ya ragu sosai, bayan sanya musu dokar dole ta ka’idar haihuwa. “Yanayin yawan al’umma a Xinjiang ya ragu sosai; yawan mutanen ya ragu da kashi 84 cikin dari daga shekarar 2015 zuwa 2018, haka kuma ya kara sauka a shekarar 2019,” ya ce.

“A shekarar 2020 kuwa, a yankin Uyghur raguwar al’ummar ya kai kusan babu ne ma.”

Zenz ya kara da cewa binciken ya nuna damuwa akan ko kasar ta China ta kakabawa mutanen wadanda da basu da rinjaye a kasar wannan doka.

Rahoton ya yi kira da fara gabatar da bincike akan tauye hakkin ‘yan adam da gwamnatin kasar China take yi.

Wata kungiya da ta hada da manyan ‘yan siyasa daga Arewacin Amurka, yankin Turai da kasar Australia, ta ce dole ne duniya ta fito tayi magana akan wannan cin zarafi da kasar ta China take yi.

Lokaci yayi da Musulmai za su yi zanga-zanga su tashi tsaye akan gwamnatin kasar China, sannan su gabatar da zanga-zanga a ko ina a duniya kamar wacce ake yi ta ‘Black Lives Matter’ a sanyawa mata take mai suna ‘Muslim Lives Matter’. Abun babu dadi ace Musulmai sun yi shiru suna gefe suna kallon bidiyo suna jin dadinsu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here