Gwamnatin jihar Kano ta amince al’umma su gabatar da sallar Juma’a da sallar Idi

0
118
  • Gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ta amince da al’umma su fita sallar Juma’a da ta Idi
  • Gwamnatin ta bayar da wannan sanarwar ne a jiya bayan gwamnan ya gana da Malaman addini a jihar
  • Gwamnatin ta amince da hakan a bisa sharadin dole mutane su bi dokokin da ta gindaya domin rage yaduwar cutar Coronavirus a jihar

Gwamnatin jihar Kano ta amince mutane su gabatar da sallar Juma’a da ta Idi a fadin jihar, a yayin da gwamnatin tarayya ta tsawaita dokar hana fita.

Sanarwar dai ta fito daga bakin gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje bayan ya gana da kungiyar Malaman addinin Musulunci dake Kano a jiya Litinin.

Sanarwar wacce ta fito daga wajen mai bawa gwamnan shawara ta musamman a fannin sadarwa, Malam Salihu Tanko Yakasai, ya ce Ganduje ya amince mutane su gabatar da sallar Juma’a da kuma sallar Idi bayan ya gana da manyan malaman addinin Musulunci a gidan gwamnati.

“Mai girma gwamna, Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya amince a zabi manyan malamai guda 30 a jihar Kano da zasu gabatar da sallar Juma’a da kuma sallar Idi a jihar.

“Wannan na nufi cire dokar hana fita a ranar Litinin da Alhamis za ta cigaba da aiki, haka kuma za ayi sallar Juma’a da sallar Idi a jihar,” cewar sanarwar.

A yadda sanarwar ta nuna, an bukaci limamai da su tabbatar da kowa ya sanya takunkumin fuska, sannan kuma kowa yayi amfani da abin wanke hannu.

Haka kuma a gabatar da Huduba takaitacciya, sannan abi dokar nisanta da juna.

Idan ba a manta ba a ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Najeriya bata shirya dawowa yadda ya kamata ba, hakan yasa dole a dauki doka mai tsauri a kasar.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha shine ya bayyana haka a wajen taro akan cutar Coronavirus na 33 da aka gabatar a Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here