Gwamnati ta bawa mutumin da ya hana danshi shiga gida saboda gudun daukar Coronavirus babban mukami

0
107

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya bawa mutumin nan da bidiyonshi yake ta yawo a shafukan sadarwa, wanda ya hana danshi da ya dawo daga kasar waje shiga masa gida saboda gudun daukar cutar Coronavirus babban mukami.

Gwamnan ya bawa mutumin mukamin Jakadan yaki da cutar Coronavirus na jihar Ekiti.

Mutumin mai suna Mr. Adeoye, wanda yake tsohon ma’aikacin hukumar kiyaye hadura ne, ya hana danshi shiga masa gida, saboda ganin cewa jirginshi ya tsaya a jihar Legas ne, kuma Legas ita ce jihar da tafi ko’ina yawan masu dauke da cutar a Najeriya, inda yake ganin cewa akwai yiwuwar ya kamu da cutar.

Gwamnatin jihar ta bayyana bashi mukamin a shafin Twitter a jiya Alhamis da yamma, inda ta bayyana cewa Mr Adeoye, yana daya daga cikin irin mutanen da jihar Ekiti take so domin samun cigaba.

“A yau na bawa Mr. Adeoye mahaifin saurayin da ya shigo jihar Ekiti ba tare da sannin hukumomi ba, mukamin Jakadan yaki da cutar Coronavirus na jihar Ekiti. Ina matukar alfahari da Mr Adeoye, kuma munji dadi da kokarin da yayi na kare jihar Ekiti.

“Mr. Adeoye zai taimaka wajen yada sakonni a matsayin shi na daya daga cikin ‘yan kungiyar masu yaki da cutar Coronavirus na jihar Ekiti.”

Haka kuma gwamnatin jihar ta bayyana cewa za ta karrama Mr. Adeoye a nan gaba akan gudummawar da ya bawa jihar Ekiti wajen ganin an samu wanzuwar zaman lafiya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here