Goddy Anabor: Hamshakin mai arziki dan Najeriya da ya talauce ya koma hayar mota

0
3157

Hamshakin mai arziki dan Najeriya mai suna Goddy Anabor da yayi tashen kudi a baya, yanzu na fama da kanshi wajen neman na abinci yau da kullum.

Goddy Anabor, wanda a yanzu haka yake yin hayar mota don samun na abinci, a baya hamshakin dan kasuwa ne, wanda ake yiwa lakabi da Ikeja Axis.

A wata hira da Anabor yayi da Bodun Kupoluyi, ya bayyana yadda ya talauce duk da tarin dukiyar da yake da ita a baya.

Tsohon mai arzikin ya bayyana cewa ya taimakawa mutane har uku suka yi arziki sosai ta sanadiyyar shi, amma bayan ya talauce duka suka juya masa baya.

A cewar shi, ya samu wannan arziki ne ta hanyar kasuwanci da ya dinga yi, amma kuma ya talauce ne saboda mutanen dake karkashinsa da suka dinga cin amanarsa suna sace kudaden shi.

Goddy Anabor ya bayyana cewa matar shi ta biyu Anthonia tayi amfani da kudin kasuwancin shi wajen rabawa mutane.

Da yake bayyana yadda ya hadu da Anthonia, ya ce ya hadu da ita a ofishin ‘yan sanda a lokacin da wani rikici ya hado su ita kuma a lokacin jami’ar ‘yan sanda ce.

Anabor ya ce ya sayar da kadarorinshi baki daya, ya sayar da gidanshi wanda kudin zai kai naira miliyan 300 akan kudi naira miliyan 84 ga Basorun A.K. Tsohon mai kudin ya bayyana cewa ya sayar da jirgin shi da kuma motocin sama da guda 50 da suka hada da Bentley, Rolls Royce da sauransu.

Duk da yanzu ya talauce bashi da ko asi, amma ya ce yana jin dadin maganganun da mutane ke yi a kanshi yanzu tun kafin ya mutu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here