Giya na sha tayi mini karo shi yasa nayi mata fyade – Cewar saurayin da ya yiwa tsohuwa fyade

0
486

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Ogun ta bayyana samun nasarar cafke wani mutumi mai shekaru 25 da suna Wasiu Bankole da laifin yiwa wata tsohuwa ‘yar shekara 70 fyade.

Rahoton da jaridar Daily Trust ta samo a garin Abeokuta ranar Alhamis daga wajen jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce sun cafke mai laifin a ranar 3 ga watan Yuni.

Oyeyemi ya ce sun samu nasarar cafke mai laifin bayan tsohuwar ta kai karar shi ofishin su dake Agbado.

Ya ce tsohuwar ta bayyana musu cewa a lokacin da take bacci a gidanta dake Abule Lemode da misalin karfe 8 na yamma, mutumin ya shiga gidanta, inda ya bita har daki, ya danne ta yayi lalata da ita ba tare da amincewarta ba.

“Matar ta bayyana cewa daya daga cikin makwabtanta ne ya jiyo lokacin da take ihu, inda ya garzayo ya ceto ta, ta hanyar amfani da ice ya daki mutumin, bayan jin zafin duka sai ya daga ta ya ranta ana kare ya bar kayan shi a cikin dakinta.

“Bayan ta kai kara, sai DPO na wannan ofishin SP Kuranga Yero ya aika da jami’an ‘yan sanda su nemo mutumin.

“Cikin sa’a ‘yan sandan sun samu nasarar kamo mai laifin a cikin awanni 24 suka kai shi ofishin ‘yan sandan,” cewar sanarwar da jami’in ya bawa Daily Trust.

Oyeyemi ya bayyana cewa bayan gabatar da bincike akan mai laifin ya bayyana cewa yayi mata fyaden ne bayan giya da ya sha tayi masa karo.

Ya ce tuni an garzaya da tsohuwar zuwa asibiti domin duba lafiyarta.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson, ya bayar da umarni a mika wanda ake zargin zuwa sashen masu safarar mutane da cin zarafin yara, domin cigaba da yi masa bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here