Gida bai koshi ba: Kasar Chadi na rokon Najeriya ta bata wutar lantarki

0
677

Gwamnatin kasar Chadi ta aiko da sako na musamman ga gwamnatin Najeriya, inda ta roki Najeriya ta bari ta hada wutar kasar da ta Najeriya.

Jakadan kasar Chadi dake Najeriya, Abakar Saleh, shine ya gabatar da wannan bukata yayin wata ziyarar aiki da ya kai wa ministan wuta, Injiniya Sale Mamman a Abuja.

Jakadan ya nuna matukar bukatar wutar lantarkin a lokacin da yake gabatar da bukatar, jakadan ya jaddada muhimmin tarihi da karfafa tattalin arziki hada wutar lantarkin zai kawo ga kasashen guda biyu.

Da yake mayar da martani akan wannan bukata, Injiniya Mamman yayi maraba da wannan cigaba, inda ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ministan ya ce bukatar kasar ta Chadi ta zo a daidai lokacin da ta dace yayin da yake tabbatarwa jakadan kasar ta Chadi cewa Najeriya za tayi duba akan wannan bukata.

“Saboda haka ina umartar kamfanin wutar lantarki na Najeriya, wanda wakilansu suke wannan taro, da su zo da mafita akan wannan cigaba, akan haka zamu aikawa da shugaban kasa sako don ya sanya hannu akan duk abubuwan da suka dace,” cewar Injin Injiniya Mamman.

Ya kuma sanar da wakilin na kasar Chadi cewa, a halin da ake ciki yanzu, akwai yarjejeniya tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar da kuma Jamhuriyar Benin ta wutar lantarki, wacce aka shafe shekara shekaru ana yi.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here