Gaskiya ta bayyana: Kasar Amurka ta siye duka maganin Coronavirus, ta bar kasashen duniya ko oho

0
497

Ma’aikatar lafiya ta kasar Amurka ta siye maganin corovirus na remdesivir na nan da kimanin wata uku, inda ta bar sauran kasashen duniya babu maganin daga nan zuwa watanni uku masu zuwa.

Gwamnatin Donald Trump ta siye maganin guda 500,000 na Remdesvir daga wajen Gilead, hakan na nuni da cewa kasar ta Amurka ta saye kashi 90 cikin dari na maganin wanda kamfanin zai iya yi daga nan zuwa watan Satumba.

Da farko dai an raba magungunan guda 140,000 ga kasashen duniya domin gabatar da gwaji, inda sai a yanzu bayan gabatar da gwajin aka gano cewa maganain yana aiki.

Da farko dai kamfanin ya kirkiri maganin a matsayin maganin Ebola, amma ganin yadda maganin yake maganin cutar COVID-19, inda aka gano cewa masu cutar da aka bawa maganin suna warke cikin gaggawa fiye da sauran magungunan.

Sakataren lafiya na kasar Amurka, Alex Azar ya yabawa kasar da sayen maganin da tayi:

“Shugaba Trump yayi aiki mai kyau da ya saye maganin wanda zai taimakawa ‘yan kasar Amurka su warke daga cutar ta COVID-19.

“Za mu tabbatar da cewa duk wani dan Amurka da yake bukatar maganin remdesivir zai samu. Gwamnatin Trump za tayi bakin kokarinta kan mutanen kasar Amurka don tabbatar da lafiyar su.

Likitan kasar Ingila, Dr Andrew Hill na jami’ar Liverpool da yake sharhi akan saye maganin da tayi, inda ya ce: “Sun saye duka maganin na remdesivir, babu abinda ya rage ga yankin Turai.”

“Remdesivir na Gilead ne, hakan na nufin babu wani kamfani da zai iya yin maganin.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here