Garin Bijagos: Kauyen da mata suke mulkar maza kuma suke zabawa kansu mazajen da za su aura

0
122
  • Wani kauye a kasar Guinea Bissau mai suna Bijagos Archipelago kauye ne da mata ke mulkar maza
  • Kauyen yayi suna wajen mafarauta, haka mata a garin an basu damar su zabi mijin aure, inda maza suke yin shiga ta kawa don jan hankalin matan
  • Haka kuma mace ce ke mulkar garin, domin kuwa al’adar garin bata bari namiji yayi mulki

Labarin Bijagos Archipelago, garin dake kasar Guinea Bissau, yayi kaurin suna a yankin, inda kowanne abu a yankin mata ne suke da iko a kai.

A wannan kauyen kamar yadda rahotanni suka nuna, mata ne suke da ikon zabar miji, sannan kuma sune suke yanke hukunci, suke lura da harkar tattalin arziki, jin dadin jama’a sune suke jagorantar mutane wajen ibada, hatta sarautar garin mace ce ke yi.

Mutanen garin dai sun shahara matuka wajen farauta, inda suke hawa wani jirgin ruwansu da yake iya daukar mutane 70 a lokaci daya.

Yawan mutanen garin ya kai mutum 25,000, inda yawancinsu matsafa ne, saboda yawan albarkatunsu ya saka UNESCO ta bayyanasu a matsayin wajen rayuwa a shekarar 1996.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here