Ganduje ya zama gwamnan da yafi kowanne iya yaki da cutar COVID-19 a Najeriya

0
959

Darakta Janar na cibiyar kula da manyan cututtuka ta Najeriya (NCDC) Dr Chikwe Ihekweazu, ya bayyana cewa jihar Kano ita ce jihar da aka fi samun masu cutar coronavirus a makon da ya gabata, hadakar kungiyar Afrika dake yaki da cutar COVID-19 ta jinjinawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje akan wannan nasara da ya samu.

Wannan yabo ya fito ne a wata takarda da aka aikowa da Ganduje mai dauke da sa hannun babban jami’in kungiyar John Kumasi Attah, a jiya Juma’a 26 ga watan Yuni, 2020.

Yabon, a cewar sanarwa da sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Malam Abba Anwar, ya fitar a safiyar yau, ya ce ya fito cikin awa 24 bayan Ihekweazu ya yabawa jihar Kano akan kokarin da tayi na yaki da cutar a Najeriya fiye da kowacce jiha a makon da ya gabata.

Ihekweazu ya bayyana hakane a wajen taron kwamitin gudanarwa na gwamnatin tarayya kan cutar COVID-19, da aka gabatar a ranar Alhamis 25 ga watan Yuni, a Abuja.

“Mun yi farin ciki sosai akan irin kokarin da gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje yayi akan annobar COVID-19. Tun lokacin da gwamnan yayi bayani kwanakin da suka gabata, akan yadda Kano ke samun nasara akan cutar, mun san duka masu ruwa da tsaki suna kallo,” cewar takardar.

A cewar wasikar, NCDC ta tabbatar da kokarin jihar Kano, dangane da mafi yawan gwaje-gwajen da aka gudanar a jihar, “ba wani abun mamaki bane idan aka yi la’akari da irin kokarin da da gwamnan jihar yayi.

“Hanyar da Ganduje yabi wajen yaki da cutar ba wai abin misali bane kawai, abu ne na goyon baya,” cewar takardar.

Wasikar ta kara da cewa: “Muna iya ganin yadda jihar Kano ke jagorantar yaki da wannan cutar. Mun san hanyoyi da dabarun COVID-19 ana kwafar su daga jihar Kano. Irin wadannan abubuwa sun hada da rufe iyakokin jihar, tare da cibiyoyin gargajiya, tare da sake horar da ma’aikatan kiwon lafiya, har ya zuwa lokacin da jihar ta zama cibiyar horarwa ta Arewacin Najeriya, da dai sauran abubuwa da yawa.”

Haka kuma sun gano cewa saboda kokarin da jihar Kano tayi wajen yaki da cutar ne ya saka da yawa daga cikin masu ruwa da tsaki suka tashi domin taimakawa jihar ta kowacce hanya.

Kungiyar a karshe ta bukaci Ganduje ya cigaba da kokarin da yake yi, inda suka ce al’ummar jihar Kano na cin ribar abinda yake yi, ba wai iya a Najeriya kawai ba, hatta kasashen Afrika suna koyi dashi.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here