Ga irinta nan: Najeriya na asarar dala biliyan 29 a kowacce shekara saboda rashin wutar lantarki – Ahmad Lawan

0
392

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, a jiya Litinin 15 ga watan Yuni, ya bayyana cewa Najeriya na asarar dala biliyan 29 ($29b) a kowacce shekara saboda matsalar wutar lantarki.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayyana cewa za a fara gabatar da bincike akan matsalar wacce aka sanyawa suna: “Tsarin dawo da wutar lantarki da tasirin annobar COVID-19”, wanda kwamitin majalisar dattawan ta wutar lantarki ta hada a Abuja.

Kwamitin ta ce gwamnati ta kashe kimanin naira tiriliyan 1.8 a fannin wutar lantarki tun shekarar 2015, amma har yanzu babu wata tsayayyiyar wutar lantarki.

Yayi kira da ayi duba akan barin wutar lantarkin a hannun ‘yan kasuwa da gwamnatin tarayya tayi, inda ya ce har yanzu babu wani cigaba da aka samu a bangaren wutar lantarkin, inda hakan ya sanya Najeriya take asarar kudaden shiga a kowacce shekara.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Lawan ya kara da cewa, yarjejeniyar da aka yi da gwamnatin tarayya da kamfanonin rarraba wutar lantarki na (DisCos) da (GenCos), shine kamfanonin sune suke da alhakin daukar asarar naira biliyan 12 zuwa 15 a kowanne wata.

Ya ce:

‘Mu dai a nan majalisa musamman majalisar dattawa, mun damu matuka. Kuma na san duka mun san dalilin da ya sanya Najeriya har yanzu ta kasa samun cigaba, musamman idan muna magana a bangaren masana’antu, da sauransu. Najeriya baza ta iya gasa da kowacce kasa ba.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here