Fitattun mawakan Najeriya sun sanya ranar da zasu gabatar da zanga-zanga akan gwamnatin Buhari

0
831

Fitacciyar mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage tayi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayan kungiyar mawaka ta kasa domin yin zanga-zanga akan gwamnati mai mulki da irin mulkin da ake gudanarwa a kasar.

Da take wallafa sanarwar a shafinta na Instagram, Tiwa Savage tayi kira ga duka ‘yan Najeriya da sauran mawaka irinta da su dakatar da duk abinda suke yi a ranar Talata 2 ga watan Yunin shekarar 2020, su hadu suyi zanga-zanga da zai saka a samu canji a Najeriya.

Ta ce: “Sanadiyyar abubuwan da suka dinga faruwa a ‘yan kwanakin nan, ku goya mana baya a yayin da zamu tashi tsaye wajen neman canji da cigaba.

“A matsayinmu na masu koyar da al’ada, nauyi ne a kanmu mu kamar yadda muke fitowa muyi murna a lokacin da aka samu cigaba, mu kuma fito mu nuna rashin jin dadin mu a lokacin da aka samu matsala, dole mu hada kan mu.

“Ku shigo cikin mu ranar Talata 2 ga watan Mayu, ku dakatar da duka abubuwan da kuke ku tashi tsaye a wannan rana.

“#THESHOWMUSTBEPAUSED”

Source: Tiwa Savage Instagram Page

Wannan dai na zuwa ne a dan lokacin da manyan mawakan irinsu Banky W, MI Abaga da Davido suka yi Allah wadai da gwamnatin Najeriya, shafukan sadarwa, da yanayin zabe a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here