Fitaccen mawakin Amurka, Kanye West ya jawo hankalin mutane da dama, bayan ya bayyana kudurinshi na fitowa takarar shugabancin kasar Amurka.
Kanye West ya bayyana hakane a shafinsa na Twitter, inda ya ce zai fito takarar a wannan shekarar ta 2020.
Kanye West dai zai kara da shugaban kasar Amurka na yanzu Donald Trump da kuma abokin hamayyarsa, kuma tsohon mataimakon shugaban kasar Amurka Joe Biden.
Mawakin kuma shugaban kamfanin takalma na Yeezy, yayi rubutun kamar haka a shafinsa na Twitter:
“Yanzu dole mu gane alkawarin Amurka ta hanyar yadda da Allah, hada kai da kuma gina rayuwar mu don gaba. Zan fito takara shugaban kasar Amurka a shekarar 2020.“
Har yanzu dai ba a tabbatar idan da gaske ne mawakin zai fito takarar shugabancin kasar, watanni hudu kafin a gabatar da zaben ba, ko kuma ya cika wata takarda da za ta sanya a barshi ya fito takara a wannan shekarar.
A ranar 3 ga watan Nuwambar shekarar nan ne dai za a gabatar da zaben shugabancin kasar ta Amurka.
Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:
Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa
Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa
YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com