Duniya ina zaki damu: An tsinci jaririya sabuwar haihuwa da aka jefar a cikin bola a jihar Neja

0
532

Wani likita mai suna Bright Oris, ya wallafa labarin yanda wani jami’in dan sanda ya tsinci jariri sabuwar haihuwa an jefar dashi a cikin bola a jihar Neja, inda yayi gaggawar kaishi asibitin da likitan yake aiki.

A cewar shi ‘yan sandan da suka tsinci jaririn wadanda suke aiki da rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja, sun jiyo kukan jaririn a cikin bola, sai suka bi sautin kukan.

Cikin gaggawa sduka garzaya da ita zuwa asibiti bayan sun ganta domin a duba lafiyarta.

Dr. Oris ya ce jaririyar lafiyar ta lau. Ga dai labarin da likitan ya wallafa a shafinsa na Twitter:

“Wannan rayuwar akwai abin dubawa a cikinta. Awa daya da ta wuce motar ‘yan sanda ta shigo cikin asibiti, sun ce sun tsinci wata jaririya a cikin shara, sai suka dauketa kuma suka saka ta a bayan motar su.

Ya kara da cewa:

‘Bayan ganin jaririyar a bayan mota a cikin leda ko cibiya ba a gama cire mata ba, sai nayi gaggawar duba yarinyar domin ceto rayuwarta. Jikinta duk yayi sanyi. Hakan na nufin yarinyar ta jima a cikin wannan bola a cikin ruwa.

“Amma jaririyar na da karfin hali!

“Mun kammala goge mata jikinta, sai muka yi kokarin jin ta bakin jami’an hukumar ‘yan sandan da suka kawo ta.

Hoton jaririyar a lokacin da take asibiti Source: @Doctorr_Bright Twitter Page
Hoton jaririyar a lokacin da take asibiti Source: @Doctorr_Bright Twitter Page

“Mun samu mun gama duba lafiyarta, yanayin jikinta ya dawo daidai, komai ya dawo yadda yake.

“Na yanke shawarar biyan kudin maganinta har zuwa lokacin da wata kungiya ko gwamnati ta sanya hannu a lamarin.

“Ina ji kamar na cigaba da daukar nauyinta. Irin wannan kyakkyawar jaririya.

“Wane irin mutum ne kuma wane dalili ne zai saka ayi tunanin jefar da irin wannan kyakkyawar yarinya?”

Hoton jaririyar a lokacin da take asibiti Source: @Doctorr_Bright Twitter Page

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here