Duk wanda yake kare Buhari, Allah ya nuna masa mulkin Buhari – Audu Bulama Bukarti

0
2919

Fitaccen mai rajin kare hakkin dan adam, Audu Bulama Bukarti, ya nuna damuwarshi akan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, musamman a wannan lokaci da ‘yan bindiga suka sako mutane a gaba suke kashe su tamkar kiyashi.

Fitaccen lauyan wanda yake dan asalin jihar Borno, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Facebook a yau Juma’a 12 ga watan Yuni, inda yayi addu’a akan mutanen da suke nuna soyayya kuma suke kare shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ce: “Duk wanda har yanzu yake kare Buhari, Allah ya nuna masa mulkin Buhari.”

Wannan addu’a da Lauyan yayi ta jawo kace nace matuka a shafinsa, inda mutane da yawa suke ganin bai kamata a yiwa shugaba irin wannan addu’a ba, kamata yayi ayi masa addu’a sannan kuma mu talakawa mu gyara halayenmu.

Duk wanda ya ke kare Buhari har yanzu, Allah, Ya Ubangiji, Ka dandana masa mulkin Buhari.

Posted by AUDU BULAMA BUKARTI on Thursday, June 11, 2020

Daga baya Bulama ya sake wallafa wani rubutun a shafinsa na Facebook inda ya karyata maganar shugaban kasa Muhammadu Buhari, dake nuni da cewa anci karfin ‘yan ta’addar Boko Haram kuma na kwato duka garuruwan dake hannunsu.

Bulama ya ce: “Kwanaki kadan bayan harin da aka kai jihar Katsina da Borno, wanda aka kashe sama da mutane 130 a cikin kwana daya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce anci karfin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a Najeriya, sannan kuma duka garuruwan dake hannun ‘yan Boko Harama an kwato su, mutane sun koma ciki da zama, wannan maganar ba gaskiya bace.

“Boko Haram ta samu koma baya sosai a lokacin mulkin Buhari na farko, amma a yanzu tana dawowa da karfinta. ‘Yan ta’addar sun kai mummunan harinsu a Najeriya, Nijar da Chadi a watan Disambar shekarar 2019. Gaskiya ne yawancin kananan hukumomin dake hannun kungiyar an kwato su, amma wasu daga ciki har yanzu suna hannunsu.

“Bayan haka, yawancin garuruwan da aka kwato har yanzu babu mutane a ciki, saboda babu tsaron da mutane za su koma ciki da zama, kuma ba a gyara su ba. Saboda haka yawancin wadanda suka tsira suna nan babu gidajen zama. Harin da aka kai na Gubio da suka kashe mutane 81 ya tabbatar da dalilin da yasa mutane basu son komawa garuruwan.

“Ta’addanci a yankin arewa maso gabas na kara karfafa a wannan lokaci na mulkin Buhari. Yanzu suna abinda suke so ba tare da wani hukunci ba kwanan nan sun kai mummunan hari, wanda yayi sanadiyyar zanga-zanga a jiharsa ta Katsina a jiya.

‘Wannan cin mutunci da rashin adalci ga mutanen da wannan abu ya shafa a ce musu ta’addanci ya ragu. Ko dai Buhari bai san abinda yake cewa ba, ko kuma yana nuna rashin gaskiya. Ina ganin rashin gaskiyar ne, saboda a matsayin shi na shugaban kasa, nauyi ne a kanshi ya san cewa ana kashe ‘yan Najeriya kamar kiyashi a kowacce rana.

Days after attacks in Borno and Katsina killed over 130 Nigerians in one day, Pres. Buhari said insurgency and banditry…

Posted by AUDU BULAMA BUKARTI on Friday, June 12, 2020

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here