Dole sai mun bi koyarwar Annabi Muhammad (SAW) idan har muna son kawo karshen ta’addanci – Shugaban addinin Buddha

0
7383

Tenzin Gyatso, wanda yake shine Dalai Lama na 14 a yanzu, kuma fitaccen marubuci, ya bayyana Al-Qur’ani mai girmda a matsayin littafi mai alfarma, wanda kyauta ce mai girma Allah ya aikowa al’ummar duniya.

Shugaban ya bayyana wannan ra’ayi nasa a wajen babban taron addinin Buddha. Jagoran ya yaba da ayyukan da Annabi Muhammad (SAW) ya yiwa al’ummar duniya.

Ya ce: “Rayuwar Annabi Muhammad (SAW), ita ce babbar misali ga dukkan al’ummar duniya. Ya kamata mu bi tafarkin da Annabi Muhammad (SAW) ya nuna domin samar da zaman lafiya sannan kuma a kawo karshen ta’addanci a duniya. Annabi Muhammad (SAW), ya koyar da zaman lafiya, kaunar juna, ya koyar da adalci da hakuri da addini, inda hakan ya kasance haske mai dorewa ga dukkan al’ummar duniya.

Dubunnan mabiya addinin Buddha daga ko’ina a fadin duniya sun samu halartar wannan taron a wajen bautarsu dake garin Bylakuppe.

Dalai Lama ya sake nanata batun cewa babu ta’addanci a addini, wadanda basu da hali mai kyau ne suke amfani da addini suke aikata ta’addanci.

Ya ce babu wani abu wai shi “Ta’addanci a Musulunci”, inda ya ce duk wani wanda yake aikata ta’addanci to ba cikakken Musulmi bane.

Shugaban ya ce duka addinan duniya a baya sun kasance masu hadin kai da nuna soyayya ga juna, ya bayyana cewa wannan hanya ce za abi domin tabbatar da zaman lafiya a duniya.

“Dan ta’addar Buddha, dan ta’addar Musulmai, wannan duk ba daidai bane. Duk wanda yake aikata ta’addanci wannan ba cikakken Musulmi bane ko dan addinin Buddha, saboda koyarwar Musulunci ne da zarar ka shiga zubar da jini, to tabbas ka fita daga cikin masu koyi da addinin Musulunci.

“Duka manyan al’adun addini suna bayar da sako iri daya ne: kauna, tausayi, afuwa, hakuri, kamewa da sauransu.

Ya bayar da hujjar cewa rarrabewa tsakanin masu tsattsauran ra’ayi da Musulmai na kwarai ita ce babbar hanyar da za a kawo karshen ta’addanci kuma a samu hadin kai.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here