Dole makarantu su bude wuraren killace dalibai kafin mu bari a cigaba da karatu – Gwamnatin tarayya

0
317

Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta ce dole ne makarantu su kirkiri wuraren killace mutane, sannan kuma su samar da wuraren duba marasa lafiya kafin a bude su.

Wannan ya zo ne a wasy sharudda na bude makarantu bayan kulle su da aka yi sanadiyyar cutar COVID-19, wanda aka aikawa majalisa a ranar Talata 22 ga watan Yuni.

A cewar sharuddan, kowacce makaranta za ta kirkiri wajen killace mutane da kuma dan karamin waje na duba marasa lafiya kafin a bude makarantar.

Haka kuma ana bukatar makarantu su samar da hanyar da za su lura da dalibai, malamai, da sauran ma’aikatan makaranta idan suka kamu da rashin lafiya a makaranta.

Ma’aikatar ta ce a cikin takardar duk wata jiha da take son bude makaranta dole ta tuntubi kwamitin gudanarwa ta gwamnatin tarayya domin bada shawarwari.

Haka kuma sharuddan sun bukaci makarantun su dauki karin ma’aikata da za su tabbatar da cewa dalibai sun bi dokar tazara ta mita 2 tsakaninsu a cikin aji.

Haka kuma ta bukaci makarantun da su samar da sabulu da bokiti, su tabbatar da samar da ruwa a kowane lokaci, sannan su samar da kayan koyon karatu, su kuma biya albashi akan lokaci.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here