Dole a raba maganin cutar Coronavirus ga kasashen duniya kowa ya samu – Cewar shugaban Kiristoci na duniya

0
186

Shugaban addinin Kiristanci na Katolika, Pope Francis, yayi kira ga masana kimiyya na duniya da su bayar da hadin kai domin kowacce kasa ta duniya ta amfana da maganin cutar Coronavirus idan an same shi.

Pope wanda yake magana a babbar cocin Vatican a jiya Lahadi lokacin da yake gabatar da wa’azi, ya ce duk maganin da aka samu aka kirkiro dole a raba shi ga kasashen duniya kowa ya samu.

Pope ya yiwa duka mutanen duniya da suke taimakawa da karfinsu da dukiyarsu wajen tallafawa al’umma.

“Ina ganin yana da matukar muhimmanci mu hada kai wajen neman maganin a bayyanashi ga al’umma domin kowa yasan halin da ake ciki,” ya ce.

“Haka kuma yana da matukar muhimmanci a bawa duk wanda yake dauke da cutar damar ayi masa magani a duk inda yake a duniya.”

Ya zuwa yanzu dai cutar ta Coronavirus ta kama kusan mutane miliyan 3.5 ta kuma kashe sama da mutum 240,000 a fadin duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here