Diezani ta samu babban mukami tare da takardun zama ‘yar kasa a Dominica, yayin da gwamnatin tarayya ke nemanta ido rufe

0
512

An bawa tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison Madueke, mukamin kwamishinar kasuwanci a kasar Dominica, inda firaministan kasar Roosevelt Skerrit ya bata wannan mukami.

Wannan mukami dai ba wani abu za ta samu mai tsoka da shi ba, cewar firaministan.

Wannan dai na zuwa ne bayan kasar ta Dominica ta bata takardar zama ‘yar kasa, kamar yadda The Nation ta ruwaito a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015, kamar yadda takardar da firaministan ta nuna.

Haka a ranar 21 ga watan Mayu Legit.ng ma ta ruwaito cewa Diezani ta samu takardar zama ‘yar kasa.

Kowa dai ya san EFCC na neman Diezani ruwa ajallo, bayan kamata da laifin sama da fadu da N23.29b.

Haka hukumar yaki da cin hanci tana zargin tsohuwar ministar da laifin sace N47.2b; $487.5m; N23.4b; da kuma $5m.

Sai dai wannan mukami da kuma takardun zama ‘yar kasa da kasar ta Dominica ta bata ya kawo koma baya sosai a kokarin da hukumomin suke yi na kamo ta.

Rahotannin wasu majiyoyi sun bayyana cewa, tsohuwar ministar tana amfani da wannan dama da ta samu a kasar Birtaniya da kuma kasar ta Dominica inda ta zama ‘yar kasa.

“Ba za mu iya kamo ta ba ba tare da kasashen guda biyu sun sanya baki ba. Ta riga ta gama shirya komai dan hana kamata. Yayin da NCA ta bayyana cewa tana cigaba da bincike akan zargin da muke yi mata, haka kuma kasar Dominica ba ta da niyyar barinta ta dawo Najeriya.

“Abinda ya rage mana yanzu shine mu kammala bincike mu bawa NCA sakamakon binciken da muka samu,” cewar majiyar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here