Dare daya Allah kanyi Bature: Mai ‘ya’ya 30 ya zama biloniya a rana daya bayan ya sayar da wasu duwatsu guda 2

0
451

Wani mai karamar masana’antar tono ma’adanai a kasar Tanzaniya ya zama babban miloniya a dare daya bayan ya sayar da wasu duwatsu guda biyu masu daraja da aka bayyana cewa sune aka taba samowa masu irin wannan girman.

Mutumin mai suna Saniniu Laizer, ya samu dama miliyan uku da digo hudu ($3.4) kimanin naira biliyan daya da dubu dari hudu a kudin Najeriya, ya sayar da duwatsun masu nauyin kilogiram 9.2 da kuma kilogiram 5.8.

A wani rahoto da BBC ta fitar, Laizer ya samo duwatsun a makon da ya gabata, amma ya sayar da su a ranar Laraba 24 ga watan Yuni, a yankin Arewacin Manyara.

“Mayar da hankali, jajircewa, aiki tukuru da kuma daidaito sune sirri na, ina godiya ga kowa da kowa,” ya ce a shafinsa na Twitter.

Mutumin mai shekaru 52 da yake da mata hudu, sannan kuma da ‘ya’ya 30, ya ce zai yanka daya daga cikin shanunsa domin murnar wannan nasara da ya samu.

Ya ce zai yi amfani da kudin nashi wajen gina makaranta da katafaren shago a kauyen na Simanjiro dake Manyara.

“Ina so na gina katafaren shago da makaranta a kusa da garina. Akwai mutane da yawa a nan da basu da kudin da za su kai ‘ya’yansu makaranta.

“Banyi karatu ba, amma ina so komai ya tafi yadda ya kamata. Ina so ‘ya’yana su tafiyar da komai yadda ya kamata,” ya ce.

Shugaban kasar John Magufuli, wanda a shekarar 2015 yayi alkawarin kare kasar akan hakar ma’adanai, ya kira Laizer yayi mishi murna.

“Wannan riba ce ta mai karamar masana’anta, hakan ya tabbatar da cewa kasar Tanzania tana da arziki,” inji shugaban kasar.

A shekarar 2017, shugaban kasar ya umarci sojoji su gina katanga mai tsawon kilomita 24 da ta kewaye wurin da aka yi imanin shine kadai a duniya da ake iya samun irin wannan dutse, a kusa da tsaunin Kilimanjoro.

Bayan shekara daya kuwa, an samu karin kudin shiga sosai a kasar ta Tanzania. Wannan kuma nada nasaba da wannan katanga da aka gina da ta hana fitar da dutsen ta barauniyar hanya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here