Dan shekara 70 ya yiwa yarinya ‘yar shekara 8 fyade ya bata N80 tayi shiru da bakinta

1
684

An kama wani mutumi dan shekara 70 da ake zargin ya yiwa wata karamar yarinya ‘yar shekara takwas fyade a Chanchanga dake garin Minna babban birnin jihar Neja.

Mutumin mai suna Mohammed Sani Umar (Tela) an kama shi da laifin yiwa yarinyar fyade har sau biyu kafin ya bata N80 domin tayi shiru da bakinta. Amma daga baya yarinyar ta tona mishi asiri bayan mahaifiyarta ta gano cewa akwai matsala a tare da ‘yar tan.

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, kawun yarinyar mai suna Abubakar ya sanarwa da Sahara Reporters: “Ta shafe makonni tana rashin lafiya, har yanzu ma bata samu sauki ba. Sai wata makwabciya ta bawa mahaifiyar yarinyar shawara akan ta sanya ido akan yarinyar.

“Bayan ‘yan kwanaki sai taga jini a jikin wandonta, sai take tambayarta mene ya faru.

“Yarinyar ta dauki mahaifiyarta zuwa inda mutumin yake, suna zuwa ta nuna shi da hannu.

“Yana ganin yarinyar da mahaifiyarta sai ya fara rokonsu akan su rufa masa asiri,” cewar Abubakar.

Ya kara da cewa Umar ya amsa laifinsa bayan ya ci uban bugu daga wajen wasu matasa na yankin, kafin su mika shi zuwa wajen ‘yan sanda domin cigaba da bincike.

“Mahaifiyar yarinyar ta fara kuka tana neman taimako. Inda mutane suka fara taruwa, suka shiga dashi wani gida suka yi masa dukan tsiya, sannan ya bayyana musu cewa yayi lalata da ita har sau biyu.

“Ya ce ya bata N50 da farko, sannan ya bata N30 a karo na biyu. Mun mika shi ga hannun ‘yan sanda domin a kai shi kotu a yanke masa hukunci,” Abubakar ya ce.

Iyayen yarinyar kuma sun roki ‘yan sanda da su tabbatar da anyi adalci wajen yanke hukunci, inda suka ce suna tsoron za a iya watsi da karar saboda Umar mutum ne da yake da alfarma a yankin.

DPO na ofishin ‘yan sandan ya ce za a kai karar gaban rundunar ‘yan sanda ta jiha a yau Litinin dinnan.

“Muna so ‘yan sanda su yi abinda ya kamata, saboda mutumin yana da alfarma sosai, kuma yana da mutane da suke belin mutanen da suka yi laifi aka kama su.

“Ya san manyan mutane a wannan yankin, akwai yiwuwar za su tsaya mishi su sanya ‘yan sanda su sake shi ayi watsi da lamarin.

“Tilas ‘yan sanda su tabbatar da adalci a wannan lamarin,” cewar iyayen yarinyar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here