Dan shekara 24 ya auri tsohuwar da ta raine shi mai shekaru 65, inda ya bada sadakin N2,500

0
1171

Wata tsohuwa mai shekaru 65 da aka bayyana sunanta da Mbah Gambreng da dan data raina mai suna Ardi Waras, sun angwance abinsu a yankin kudancin Sumatra, dake kasar Indonesia.

Rahotanni sun bayyana cewa Gambreng ta fara rainon Ardi shekarar da ta gabata, kuma suna zaune tare tun lokacin, duk da dai cewa ta bayyana cewa bata da niyyar aurenshi a wancan lokacin. Ta ce tayi matukar mamaki da ya nemi aurenta.

Ardi and Mbah | Photo Source: Facebook

Masoyan an daura musu aure a gaban ‘ya’yanta mata guda uku da take raino, ta ce: “abin ya bani mamaki lokacin da ya ce mini zai aure ni.”

Ardi ya biya amaryar tashi sadakin 100,000 IDR, kimanin naira 2,500 kenan a kudin Najeriya, kamar dai yadda dokar addinin Musulunci ta tanada a kasar ta Indonesia, inda ango ko mahaifin ango zai bayar da kudi ko kuma wani abu mai muhimmanci a matsayin sadaki.

Ardi and Mbah | Photo Source: Facebook

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here