Dan sanda ya bindige matashin Malamin addinin Musulunci har lahira a jihar Legas

1
312

An cafke wani jami’in dan sanda da aka bayyana sunan shi da Inspector Okoro Charles, da hannu a harbe-harben da ya faru a yankin Ikotun dake jihar Legas a ranar Laraba, 20 ga watan Mayu, inda yayi sanadiyyar mutuwar wani matashin Malami addinin Musulunci mai shekaru 28 mai suna Fatai Oladipupo.

Dan sandan wanda yake tsare a babban ofishin ‘yan sandan jihar, za a mika shi ga ofishin binciken manyan laifuka inda za su gabatar da bincike a kanshi kafin su kai shi kotu.

A rahoton da aka bawa jaridar yanar gizo ta Linda Ikeji, daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bala Elkana, ya bayyana cewa yanzu haka suna cigaba da bincike domin gano ainahin abinda ya faru dangane da harbe Malamin.

“A ranar 20 ga watan Mayun shekarar 2020, rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama Inspector Okoro Charles dake aiki a ofishin ‘yan sanda na Ikotun. An kama jami’in da hannu wajen harbe-harben da aka yi a ranar 20 ga watan 5 na wannan shekarar, a wajen Obabiyi, dake kan hanyar Igando, dake Ikotun, inda harbin yayi sanadiyyar mutuwar wani mai suna Fatai Oladipupo mai shekaru 28 a duniya dake unguwar Obabiyi.

“Yanzu haka dan sandan yana tsare a babban ofishin rundunar ‘yan sanda na jiha, za a danka shi ga ofishin binciken manyan laifuka dake Yaba domin gabatar da bincike kuma su mika shi gaban kotu.

“Muna cigaba da gabatar da bincike a yanzu domin gano ainahin abinda ya faru a wannan rana. Kwamishinan ‘yan sanda yana mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin kuma yayi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu. Inda yayi alkawarin za ayi adalci akan wannan lamari.” Cewar Bala Elkana.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here