Dan Najeriya da Baturiya ‘yar kasar Amurka ta tsinta a titi ya zama babban likita

0
3012

Wata Baturiya ‘yar kasar Amurka mai suna Melissa, ta bayar da labarin wani yaro mai suna Anejado Paul, wanda suka tsinta shekaru 18 da suka wuce a lokacin da yake fama da rashin lafiya, suka kai shi asibiti, sannan suka saka shi a makaranta, inda yanzu ya zama babban likita

Idan ka taimaki mutum daya, kamar ka taimaki baki daya mutanen kauye ko garin da wannan mutumi yake nen.

Wani yaro dan Najeriya mai suna Anejado Paul, wanda wata Baturiya ‘yar kasar Amurka mai suna Melissa ta tsinta a titi shekaru 19 da suka wuce, yanzu haka ya zama babban likita.

Baturiyar ta bayyana yadda ita da ‘yan uwanta suka hadu da Paul a wani kauye dake tsakiyar Najeriya. Ta kuma nuna yadda ta tausaya masa a lokacin da taga halin da yake ciki, kamar yadda NigerianVoice ta ruwaito.

“Iyayena sun hadu da Anejodo Paul a wani karamin kauye a cikin Najeriya shekara 18 da rabi kenan yanzu.

“Na kan fashe da kuka idan na tuna lokacin dana ganshi a kasan bishiya yana ta kore kuda daga kafarshi wacce kuraje suka cika,” ta ce.

Tare da taimakon wasu mutanen, an samu an yiwa Paul magani a wani asibiti dake Ile-Ife.

Bayan shekara daya, sai yazo yak zama a gidanmu lokacin yana da shekaru 13 a duniya, a lokacin ya fara zuwa makaranta.

A wannan makon sai ya samu labarin cewa ya samu nasarar haye jarrabawar da yayi ta likita.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here