Wani dan majalisar wakilai na tarayya, Zakariya Dauda Nyampa, ya bukaci da a dauki sababbin daliban da suka kammala karatu a Najeriya aikin soja.
Nyampa wanda yake wakiltar Michika Madagali dake jihar Adamawa, ya ce kamata yayi hukumar soja ta maye gurbin dalibai da suke bautar kasa.
Dan majalisar ya bayyana hakane a wajen wani taro na kungiyar sakai, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Ya ce duka wadanda basu son aikin sojan za su iya tafiya su nemi wani aikin bayan kammala horon a wajen sojoji.
Kwanakin baya mun kawo rahoton yadda dan majalisar dattijai na tarayya, Sanata Ali Ndume ya nuna rashin jin dadin shi akan yadda talakawan Najeriya ke cikin wani hali a wannan lokacin.
Sanatan ya ce iya ‘yan tsirarun ma’aikatan gwamnati ne kawai suke jin dadin albashin su a Najeriya, inda ya sanya kanshi a matsayin misali.
Ya ce yawancin albashin da ake bawa ma’aikata a Najeriya na kashewa ne kawai, ba zai yiwu mutum ya tara har yayi wani abu da shi a rayuwa ba.
Ba za mu taba samun kwanciyar hankali ba, saboda talakawa na cikin damuwa – Sanata Ali Ndume
Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:
Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa
Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa
YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com