Dan Allah ku taimakeni kashe ni suke neman yi – Cewar budurwa ‘yar Najeriya da aka yi safarar ta zuwa kasar Oman

0
357

Wata budurwa ‘yar Najeriya mai suna Adetomisin, wacce aka yi safarar ta daga Najeriya zuwa kasar Oman, tayi kira ga gwamnatin Najeriya akan ta taimaketa ta dawo da ita gida yayin da abubuwa suka cakude mata a kasar Oman.

A wani bidiyo da ta fito, Adetomisin wacce take magana cikin yaren Yarabanci, ta ce sunyi alkawari da wani mutumi da yayi mata alkawarin nema mata aiki a kasar Amurka. Amma komai ya canja yayin da ta tsinci kanta a kasar Oman.

“Barkan ku dai ‘yan Najeriya, sunana Adetomisin, ni ‘yar Najeriya ce ‘yar asalin jihar Ondo. Yanzu haka ina magana daga kasar Oman ne.

“A lokacin da nake shirin barin Najeriya, munyi alkawari da wani mutumi akan zai kai ni kasar Amurka ya nema mini aiki. A lokacin dana kammala karatun NCE dina kuma ban samu aiki ba, sai kawai na yanke shawarar tafiya.

“Mutumin yayi mini alkawarin sama mini aiki a kasar Amurka. Kawai sai kuma komai ya canja. Ban san mene ya faru ba, kawai sai ganin mu muka yi a Oman ni da wata budurwa. A lokacin da muka isa filin jirgi wasu mutane guda biyu suka zo suka dauke mu suka kai mu ofishinsu, suka kwace komai namu daga fasfo har wayoyin mu.

“Daga nan suka kai mu inda zamu fara aiki, sai da muka yi aikin wata hudu ba tare da an biya mu ko kwabo ba. Dana kira mutumin da ya kawo ni, sai yace shi ba ruwanshi tunda yayi iya yinshi, tun daga wannan lokacin ya daina daga kirana.

“Wanda muke yiwa aikin ya cigaba da yi mini barazanar lalata dani, ni kuma naki yarda. Tun karfe 4 na dare nake tashi bani zan kwanta ba sai 12 ko karfe 1 na dare. Har barazana ya fara yi mini idan har ban kwanta dashi ba zai kashe ni. A lokacin ne nace masa ba zanyi aikin ba, ina so na koma kasata, tunda aiki nake yi musu basa biyana.

“A lokacin suka mayar dani ofishinsu suka fara dukana. Suka kai ni wani daki suka kulle ni tare da wasu, tsawon mako guda ba tare da sun bamu abinci ko ruwa ba, yawancin mu muna shan ruwan bandaki ne, kafin daga nan suka kara kai mu muka cigaba da aiki.

“Yanzu haka shekara ta daya da wata biyu ina yi musu aiki, ga rashin lafiya da nake fama da shi. Na gayawa mutumin da muke yiwa aiki ina so na dawo Najeriya, amma ya ce a’a bazan iya dawowa Najeriya ba.

“Dan Allah ‘yan Najeriya ku taimakeni, ina so na dawo gida. Bani da lafiya kuma sunki bari na dawo. Dan Allah a taimakeni ban so na mutu a nan.” Ta ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here