Dan acaba ya kone kanshi har lahira a cikin ofishin ‘yan sanda, bayan sun kwace masa babur

0
337

Wani saurayi mai shekaru 29, mai suna Hussain Walugembe, wanda ke sana’ar acaba a kasar Uganda, ya kashe kanshi ta hanyar sanyawa kanshi wuta a cikin ofishin ‘yan sanda, a lokacin da yaje karbo babur din shi da suka kwace.

A rahoton da wata jarida ta kasar ta Uganda ta fitar, Walugembe, an kwace mishi babur a yankin kudu maso yammacin Masaka, kimanin kilomita 134 zuwa babban birnin kasar na Kampala.

‘Yan sandan sun kwace babur din a ranar 29 ga watan Yuni, a kokarin da suke na sanya mutane su bi doka don dakile yaduwar cutar coronavirus a kasar, bayan haka kuma dama gwamnatin kasar ta sanya dokar hana acaba a kasar wanda aka fi sani da Boda bodas. An lamunce musu suyi aiki ne daga karfe 6:30 zuwa karfe 5:00 na yamma, hakan iya kaya aka amince su dauka ba mutane ba.

A cewar ‘yan sanda, Mr Walugembe ya arawa abokinshi babur din shine, inda aka kama shi a lokacin da ya dauki fasinja. Ran Walugembe ya baci a lokacin da yaje ofishin ‘yan sandan, inda suka dinga sanya shi yana zirga-zirga ba tare da sun bashi babur din ba.

Ranar Alhamis 2 ga watan Yuli, ya ziyarci ofishin ‘yan sandan sai ya shiga wani daki ya kulle kanshi sannan ya sanyawa kanshi wuta a ciki. Wani jami’in dan sanda da yake tare da shi a lokacin ya samu raunika sakamakon wutar da ya kunna, haka kuma wasu takardu da na’urori masu muhimmanci sun kone.

Da yake magana akan lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, Paul Kangave, ya ce suna bincike akan lamarin, wanda ake zargin wasu daga cikin jami’an ‘yan sandan sun bukaci ya basu $32 kafin su bashi babur din.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here