Damisa ta cinye matar da take bata abinci a gaban mutanen da suka je kallonta

0
348

Wata katuwar damisa ta cinye wata mata da take kula da su a gaban mutanen da suka je kallonta a gidan ajiye dabbobi na Zurich.

Damisar da aka sanya mata suna Irina, ta kai wa matar hari a cikin gidan da aka kulleta da misalin karfe 1 na ranar 4 ga watan Yuli.

Mutanen da suka je kallo gidan ajiye dabbobin cikin tashin hankali suka sanar da halin da ake ciki.

Cikin gaggawa ma’aikatan wajen suka bazama don ceto rayuwar matar, amma ina sun makaro domin kuwa damisar ta riga ta aikata lahira, cewar kakakin rundunar ‘yan sandan Zurich, Judith Hoedl.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gidan ajiye dabbobin yayi, ya bayyana cewa: “Jami’an tsaron mu sun samu sakon cewa matar da take kula da dabbobi, wata damisa ta kai mata hari.”

Leider müssen wir euch mitteilen, dass heute im #zoozuerich eine Tierpflegerin von einem Amurtiger tödlich verletzt…

Posted by Zoo Zürich on Saturday, July 4, 2020

“Bayan zuwan su wajen sun samu nasarar korar damisar daga wajen, suka samu suka shiga wajen, sai dai kuma sun makaro domin kuwa tuni har ta riga ta mutu.”

Daraktan gidan ajiye dabbobin Severin Dressen daga baya ya sanar da manema labarai cewa: “Muna mika sakon ta’aziyyar mu ga iyalan wannan mata da lamarin ya faru da ita.

Ya ce matar ta jima tana aiki da su a wannan waje.

Irina dai an haifeta a shekarar 2015 a wani gidan ajiye dabbobi na Danish, daga baya an dawo da ita gidan ajiye dabbobi na Zurich, a cewar Dressen.

Ta maye gurbin wata damisa ne da ta mutu sakamakon fada da tayi da wata damisa ‘yar uwarta.

Gidan ajiye dabbobin da aka bude shi a ‘yan kwanakin nan sakamakon coronavirus, za a kulle daga yau Lahadi din nan.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here