Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, yayi zargin cewa jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo, sune iyayen gidan tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na kasa, Ibrahim Magu, wanda aka dakatar a makon da ya gabata.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi, ya bayyana cewa dama can Magu ba wai shugaban kasa Muhammadu Buhari yake yiwa aiki ba a lokacin da yake ofis, iyayen gidanshi kawai yake yiwa aiki.

Ya ce: “Abinda yake faruwa da Magu a yanzu, dama can an tsara shi shekaru da yawa da suka wuce. Ba wai Magu ake bi ba, ana bibiyar wadanda yake yiwa aiki ne kuma yake karewa shekaru 4 da suka wuce.

“Shi dama ba Buhari yake yiwa aiki ba. Tinubu da Osinbajo yake yiwa aiki. Idan suka gama da shi za su koma kan iyayen gidan nasa.”

Magu dai an tsare shi a helkwatar hukumar ‘yan sanda dake Abuja, akan zargin rashin gaskiya wajen tafiyar da harkokinsa a lokacin da yake jagorantar hukumar EFCC.

Ana zargin shi da laifuka masu yawan gaske da suka hada da cin hanci da rashawa, wanda ita ce babbar abinda yake ikirari akan yana yaki da shi a kasar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here