Dama can bana son Buhari shi yasa ban zabe shi ba, saboda na san babu abinda zai tsinanawa Najeriya – Tanko Yakasai

0
430

Daya daga cikin dattijan Arewa, Alhaji Tanko Yakasai, ya ce dama shi tun farko bai nuna goyon bayanshi akan Buhari ba a shekarar 2015, saboda ya san cewa babu abinda zai iya tsinanawa Najeriya.

Sai dai kuma, ya ce yayi tunanin bayan shugaban kasar ya lashe zabe zai kawo gyara koda a fannin wutar lantarki ne.

Yakasai ya ce yanzu haka shekaru biyar sun wuce, har yanzu shugaban kasar bai bashi wani kwakkwaran dalilin da zai canja ra’ayinshi akan shi ba.

Alhaji Tanko Yakasai

Fitaccen dan siyasar na jihar Kano, ya bayyana haka ne a lokacin wani taron yanar gizo da aka gabatar kan matsalolin da ake samu wajen taron yanar gizo.

“Ban taba goyawa Buhari baya ba. Dama can ni dan adawarshi ne saboda naji a jikina babu abinda zai iya tsinanawa Najeriya, kuma hakan ya zama gaskiya,” Yakasai ya bayyana haka a wajen taron wanda sama da mutum dari suka halarta.

Ya kara da cewa, “A lokacin da shugaba Buhari ya hau mulki nayi tunanin zamu samu canji koda a fannin wutar lantarki ne. Wannan ita ce shekara ta biyar da yake kan mulki. Shekaru biyu kawai suka rage masa, saboda shekara ta uku ta yakin neman zabe ce.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

“Ban san menene abinda yake so yayi ba, yaushe jihar Kano za ta samu wutar lantarkin da za ta farfado da masana’antun ta, koda kowanne mutum a jihar Kano zai samu aikin yi, haka jihohin Enugu da Lagos. Wadannan sune manyan matsalolin da suke Najeriya lokacin da aka zabi Buhari, kuma har yanzu sune dai babu wani canji da aka samu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here