Dama ba mu ce zamu cikawa mutane alkawuran zabe dari bisa dari ba – Garba Shehu

0
1141

Babban mai bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a fannin sadarwa, Malam Garba Shehu, a wani martani da ya mayar kan wata tambaya da aka aika masa a Email, ya tabbatar da cewa alkawuran da APC ta dauka a lokacin zabe ba zai yiwu Buhari ya iya cika su dari bisa dari ba.

Aminiya: Me zaka ce game da ayyukan da Buhari ya yi a ofis?

Garba Shehu: Mun gode Allah da muka ga shekara ta biyar da shugaban kasar yayi a ofis. Na ga mutane da yawa rike da wuka sun zo don taya mu murnar yanka cake, wasu kuma gaba daya sun gama shiryawa don kalubalantar mu. Daman mun san da haka, idan aka yi duba da irin rawar da shugaba Buhari ya taka a matsayinsa na jagora wanda ya samu amincewar talakawa a fadin Najeriya.

Mutumin da ya sha alwashin ceto kasarmu daga hannun ‘yan ta’adda, kawar da rashawa da kuma habaka tattalin arziki, an samu cigaba sosai a wadannan fannoni, hakan ya bashi damar samun nasara ta rike amanar mutane.

Garba Shehu da shugaban kasa Muhammadu Buhari

Duk da cewa har yanzu bamu kai inda muke son zuwa ba, amma babu shakka ba yadda muka samu kasar take ba har yanzu; mun samu babban cigaba a bangarori da dama da suka fi daukar hankalin shugaban kasar; irinsu tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Kowa dai ya san cewa ana daukar lokaci sosai kafin a samu cigaba mai dorewa.

Dole ne muyi magana ta gaskiya, mun dauki shekaru masu yawan gaske kafin mu shiga wannan hali, tun a lokacin gwamnatocin da suka gabata da lokacin akwai kayan albarkatu masu yawan gaske, ba zai yiwu ace an dawo da komai a cikin kankanin lokaci ba.

Duk wata magana da za ayi ya kamata ayi duba da yadda shugaban kasar ya riski kasar a lokacin da ya hau mulki. Dole sai an dauki lokaci kafin a samu gyara mai dorewa. Abu mafi muhimmanci shine mu nuna cewa muna kan hanya madaidaiciya, kuma kowa ya san tabbas muna kai.

Aminiya: Wadanne nasarori da matsaloli ya samu a gwamnatinsa?

Mun kammala ayyukan da yawa waɗanda gwamnatocin da suka gabata suka yi watsi da su, kuma mun fara wasu da yawa wadanda ba a dauke su da muhimmanci ba.

Gwamnatin ta kammala titin jirgin kasa mai amfani da wutar lantarki na Abuja wanda ya hada cikin gari da filin jirgin sama da kuma tashar jirgin kasa ta Idu.

Ta kammala layin dogo mai tsawon kilomita 327 na Itakpe-Ajaokuta-Warri, wanda gwamnatin tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida ta fara a shekarar 1987; sama da shekara 30 da suka wuce.

An fara layin dogo na Legas zuwa Ibadan, inda a cikin shekaru uku mun kammala aikin bin diddigin kwangilar.

Manyan ayyukan da suka rage a yanzu sune tashoshin jirgin kasa, kafofin sadarwa, da kuma sanya shinge tsakanin babbar tashar dake Ebute Metta da kuma Apapa Port Complex. Za a kammala aikin a cikin wannan shekara ta 2020.

A karshe mun samu karya lagon samar da isassun kudaden aikin gadar Second Niger Bridge da kuma babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, dukkansu ana kan hanyar kammalasu a shekarar 2022. Haka kuma hanyar da ta tashi daga Abuja-Kaduna-Zari-Kano duka ana yin aikinsu da kudin PIDF da shugaban kasa ya kafa a shekarar 2018.

A fannin aikin gona kuwa, an bayar da tallafi mai yawan gaske ga bangaren. Tsare-tsare kamar irinsu tallafin bada bashi na ‘Anchor Borrower Programme), takin shugaban kasa na zamani (PFI) da kuma kudin FarmerMoni, sun taimaka matuka wajen harkar noma.

Noman shinkafa ya ninka tun shekarar 2015. A shekarar 2019 Najeriya ta sama da tan 9.6 daga tan 4.8 da ta samar a shekarar 2015. Mun ga irin cigaban da ake samu a bangaren shinkafa, tare da sa hannun jarin sama da dala biliyan daya a sababbin masana’antu na sarrafa shinkafa a fadin Najeriya.

Mun ga yadda kamfanoni masu zaman kansu ke sanya hannun jari, da kuma gwamnatocin jihohi da suke kokari wajen harkar noma.

Gwamnatin ta kirkiro da shirin zuba jari na al’umma mafi girma a nahiyar Afrika, wanda ya kunshi shirin ciyar da dalibai, aikawa marasa karfi kudade a asusun su, daukar ma’aikatan N-Power.

Duka wadannan shirye-shirye suna da sama da mutane miliyan 13 da suke amfana da su.

Wadansu daga cikin sauye-sauyen tsarin mulki da wannan gwamnatin tayi a shekarar 2019 ya hada da sake fasalin sunan hukumar gidan yari daga Nigeria Prison Service (NPS) zuwa Nigeria Correctional Service (NCS).

Kafa asusun ‘yan sanda wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar ‘yan sandan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here